Nan gaba kadan rikicin Boko-haram zai zama tarihi -Janar Attahiru

Marigayi Janar Attahiru
Sani Gazas Chinade Daga Damaturu
Babban Hafsan Dakarun kasar nan, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, ya bayyana cewa, nan ba da jima wa ba cikin ikon Allah rikicin Boko Haram da ya dabaibaye wannan yanki na Arewa maso Gabas zai zama tarihi.
Babban Hafsan ya bayyana hakan ne a ziyarar da ya kai garin Ngamdu a jihar Borno, tare da cewa, za su hada kai da sojojin kasar Chadi domin kawo karshen mayakan Boko Haram ta ko halin kaka.
Janar din, ya jaddada hakan ne a yayin ganawar sa da manema labarai a garin Ngamdu, kafin nan sai da ya gana da jami’an sojojin da ke karkashin kulawarsa tare da yi masu alkawarin za a inganta aikinsu, da kuma samar masu kayan aiki domin magance wannan matsala ta ‘yan ta’adda; sai kuma ya tabbatar da cewa, za a share masu hawayensu a kan duk wadansu matsaloli da ke addabarsu ba tare da bata lokaci ba.
Ya kara bayyana cewar shugaban kasa na nuna matukar damuwarsa da yadda ayyukan ta’addanci ke cigaba da habaka a wannan yankin, wadda hakan Na daga cikin masudin kawo wannan ziyara ta su da nufin karfafa musu gwiwa a fafutukar da suke yi na kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu da kuma diyaicin kasar nan.
A cewarsa sabbin tsare-tsare da suka fito da su ba wai don wani abu ba ne, illa su kawo karshen wannan yakin da ake gwabzawa ne da wadannan ma su tada kayar baya na Boko Haram. Shine ma ya sa aka duba aikin rundunar sojin ta Tura Ta Kai Bango, za a ga cewar an samu nasarori da daman gaske matuka.
Don sum a halin yanzu suna son ne su dora daga inda aka tsaya akan yaki da ta’addanci da ake yi ta yadda sun daura damarar har sun ga bayansu