NARTO ta bukaci a biya ta diyya -Saboda kona tirela a Anambara

NARTO ta bukaci a biya ta diyya -Saboda kona tirela a Anambara

NARTO ta bukaci a biya ta diyya -Saboda kona tirela a Anambara

Tura wannan Sakon

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Kungiyar masu motocin haya ta Nijeriya NARTO reshen Potiskum a jihar Yobe sun roki gwamnatin jihar Anambra da ta biya diyya ga mamallakin motar nan tirela mai dauke da shanu mai lamba TO 168 YB da wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka kona a safiyar ranar Lahadi 8 ga Mayu, 2022.

Shugaban kungiyar ta NARTO, Alhaji Manga Mohammed ne ya yi rokon a yayin da yake zantawa da wakilinmu kan lamarin. A cewarsa, “Mambobinmu suna gudanar da harkokinsu na halal na sufuri zuwa yankunan kudancin kasar nan, me ya sa za a kai musu hari da kuma tsangwama, alhali Nijeriya ce kasarmu da ya kamata mu zauna lafiya da juna.”

“Mu a madadin kungiyarmu muna kira ga gwamnatin jihar Anambra da ta biya Lawan Tukur, mamallakin motar tirelar da aka kona diyya domin rage masa kuncin rayuwa. Wannan babbar motar daukar kaya na dauke ne da kayayyaki da nufin inganta tattalin arzikin jihar ta Anambra.

Don haka akwai bukatar da lalle gwamnatin jihar Anambra da ta yi hobbasa wajen jan kunnen masu irin wannan aika-aika domin gudun mayar da martini”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *