Nasarar karota, samun shugaba jajirtacce -Nasiru Na’ibawa

Baffa Dan Agundi
Daga Rabiu Sunusi
An alakanta nasarorin da hukumar kula da sifuri ta jihar Kano watau KAROTA take samu bisa samun jajirtaccen shugaba nagari da hukumar ta samu.
Hakan ya fito ne daga bakin babban mai bai wa gwamnan jihar Kano shawara dangane da hukumar, kuma tsohon shugaban karamar hukumar Kumbotso Honarabul Nasiru Usman, a tattaunawarsa da wakilinmu, ranar Litinin.
Tsohon shugaban karamar hukumar ta Kumbotso, ya ce, babu abin da yake wa Allah godiya da shi face yadda maigirma gwamna, ya yarda da shi har ya dauki wannan kujera ya ba shi a matsayin mai ba shi shawara a wannan hukuma ta Karota.
Ya kuma tabbatar dacewa, amintar da shugaban hukumar, Honarabul Baffa Babba Dan Agundi ya yi da shi ita ma ba karamar nasara ba ce, tare da amintar da su kansu ma’aikatan hukumar suka yi masa na daga cikin ci gaba mai dorewa.
Ya kara da cewa, ba shi damar da Kwamandan hukuma ya yi a yanzu, ya na ganin babu wani S.A da yake da dama kamar sa, idan ma akwai to shi yana daga cikin na sahun gaba.
Ya ce, zuwan hukumar, an sami nasarar samar da hanya mai inganci a cikin kasuwannin jihar Kano da suke fama da cinkoso a zamanin baya, amma ya zuwa yanzu cikin yardar Allah an sami sauki ta hanyar rage cinkoso mai yawa a cikin kwaryar jahar Kano da ma sauran kananan hukumomin jihar.
A cikin ci gaban dai da shugaban hukumar ya samar, Nasiru Usman ya ce, ya sama waa ma’aikatan hukumar kayan aiki, kama daga takalma da rigunan ruwa da canja masu kaki da janyo hankalin ma’aikatan wajen zuwa aiki a kan lokaci kuma koda yaushe.
Ya ce, shugaban ya bude hanyar kara bai wa jami’an Karota horo da bita kan yadda za su rinka gudanar da aikinsu, sabanin lokutan baya da jama’a ke kokawa kan ayyukan hukumar tare da tsaftar jikin jami’an da kuma kayan aikinsu.