Nasarorin Karota, kokarin Ganduje -Babba Dan’Agundi

Daga Rabiu Sunusi Katsina
An bayyana cewa, hukumar Karota ta sami nasara ta hanyar taimakon da gwamnati jihar Kano take bayarwa ga hukumar.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin babban shugaban hukumar na jiha, Baffa Babba Dan Agundi a wata tattaunawar da ya yi da manema labarai kan ayyukan karshen shekarar da ta gabata.
Dan Agundi ya tabbatar wa da manema labarai cewa, a yanzu hukumar ta sami nasarori daban-daban zuwa yanzu, wanda nasarorin sun hada da samar wa da hukumar motocin gudanar da aiki akalla guda 60 fiye da yadda ta fara da guda 3, yayin da a shekarar 2020 suka samu nasarar samar wa da hukumar motoci 50 a karkashin kulawarsa.
Haka kuma shugaban hukumar ya kara da cewa, zuwa yanzu jihar Kano tana samun ci gaba wajen bin umarnin tuki da direbobi ke bayar da hadin kai wajen tabbatar da tsari wajen ayyukansu na yau da kullun da kawo gyara da bunkasa jihar. Kwamandan Karota ya ci gaba da bayyana cewa, a shekarar 2021 hukumar ta samu nasarar daukar ma’aikata fiye da 700 yayin da kuma ta dauki na wucin gadi 300 da ya kama jimilla 1000, wannan ma babbar nasara ce.
Kazalika hukumar ta samu nasarar cafke masu laifi daban-daban da suka hada da satar mitar wutar lantarki da satar wayar lantarki da dai sauransu. Akwai aiki tare da hukumar KARMA da hukumar KAROTA ta gudanar a shekara ta 2021 kuma an cim ma nasara a kan hakan.
Kan batun ayyukan sabuwar shekara kuma, shugaban ya bukaci direbobi musamman na A-daidaita Sahu da su kokarta sabunta rajistarsu, haka kuma ya roki wadanda ba su yi rajistar ba da su kokarta yin ta ba tare da kai ruwa rana ba.
Kuma ya kara yaba wa shugaban kungiyoyin direbobi ta jihar bisa yadda suke shige da fice wajen ganin a tsabtace harkokin tuki a jihar. Dan Agundi ya ce, hukumar za ta kokarta gyaran bariyoyi da suke kan gadoji da mafi yawansu sun lalace sakamakon hawan manyan motoci da suke masu.
Haka kuma hukumar ta shirya saka launin dorawa a layin kan tituna masu falan daya da ke ciki da wajen jihar Kano domin tabbatar da an rage samun hadaruruka da ke yawaita a kan tituna cikin gari.
Shugaban ya kuma bukaci masu manyan motoci kama daga tireloli da sauransu da su kauce wa tsayawa kan titunan unguwanni, da tsayawa kan tituna babu tsari.
Game da aiki kuma, ya ce, kukumar KAROTA za ta yi aiki kafada da kafada da hukumar kare hadari ta jihar Kano watau Road Safety domin samar da daidaito ga direbobi masu shige da fice a fadin jihar.
Dokta Dan Agundi, ya kuma yi alkawarin gabatar da taron wayar wa direbobi kai da samun nasara kan ayyukansu, haka kuma ya ce, za su kuma samar da damar bayar da bita ga ma’aikatan KAROTA tare da koyar da su dabarun aiki domin ci gaban hukumar.
Kuma shugaban ya bukaci al’umma da su bayar da hadin kai ga bangaren KAROTA domin dukkan abin hukumar take yi tana yi ne domin samar da zaman lafiya ga al’ummar jihar Kano da ma kasa baki daya.
Haka zalika ya gargadi masu A-daidaita Sahu kan batun rajista da ake cewa, wadansu suna tayar da hankalin al’umma tare da ikirarin tafiya yajin aiki domin haka ya ja kunnen masu haka, idan ba su mayar da hankalinsu ba, to doka za tai aikin a kansu a wannan karon.
Dokta Baffa ya kuma nuna damuwar sa tare da alhinin rasa ma’aikatansa guda biyu a cikin shekarar da ta gabata tare da kara mika ta’aziyyar gwamnati da hukumar Karota ga ‘yan’uwa da iyalansu.
Haka kuma ya kara jajanta wa ga mutane 3 da suka samu raunuka yayin gabatar da aikinsu, tare da fatan samun lafiyarsu. Daga karshe, ya ce, hukumar tana fatan jihohin da ke fama da rashin tsaro da Ubangiji ya kawo karshen al’amarin.