Neja ta rufe makarantun kwana bayan sace daliban Kagara

Gwamnatin Jihar Niger dake Najeriya ta sanar da rufe daukacin makarantun kwanan dake kananan hukumomi 4 dake Jihar sakamakon sace daliban makarantar Sakandaren Kagara sama da 200 da Yan bindiga suka yi da asubahin yau.
Gwamna Abubakar Sani Bello ya bayyana Kananan hukumomin da umurnin ya shafa da suka hada da Munya, Mariga da kuma Shiroro.
An bayyana sunan dalibin da Yan bindigar suka harbe har lahira lokacin da suka kai hari makarantar a matsayin Benjamin Doma.
Rahotanni sun ce Yan bindigar sun harbe Doma ne lokacin da yake kokarin tserewa daga makarantar, bayan anyi garkuwa da su.
Ya zuwa yanzu dai babu rahotan dake nuna cewar Yan bindigar sun gabatar da bukatar su, yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa sojoji da Yan Sanda umurnin kubutar da daliban.