Neman goyon baya: Osinbanjo ya ziyarci Zamfara

Neman goyon baya: Osinbanjo ya ziyarci Zamfara
Tura wannan Sakon

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, jigo a jam’iyyar APC kuma mai neman tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023, ya ziyarci jihar Zamfara domin ganawar sirri da wakilan jam’iyyar APC a jihar Zamfara.

Mataimakin shugaban kasar wanda ya amsa tambayoyin manema labarai jim kadan bayan kammala taron, ya ce, ya gudanar da shawarwari mai inganci domin game da zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Ya ce, ya kuma yi tattaunawa mai inganci da sauran ‘yan jam’iyyar kan al’amuran da suka shafi hadin kan jam’iyyar a jihar.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana jin dadinsa da irin tarbar da ‘ya’yan jam’iyyar APC suka yi masa a jihar Zamfara.

Osinbajo ya kuma yi wata ganawa da majalisar Sarakunan jihar Zamfara, karkashin jagorancin Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmed. Cikin jawabinsa shugaban majalisar sarakuna na jihar Zamfara, Alhaji Attahiru Ahmed ya sake nanata rokonsa da ya yi tun farko ga gwamnatin tarayya da ta bai wa sarakunan gargajiya rawar da kundin tsarin mulki ya tanada.

Ahmed ya ce, bai wa sarakunan gargajiya rawar da kundin tsarin mulki ya tanada zai samar da zaman lafiya da tsaro a yankunansu da bin doka da oda a fadin kasar. Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta kara bai wa gwamnatin jihar goyon baya domin kawo karshen matsalolin tsaro da ake fama da su , Sarkin ya yi kira ga gwamnati da ta samar da kayan noma ga manoma.

Mataimakin shugaban kasar ya samu tarba ne a lokacin da gwamna Bello Matawalle, da tsohon gwamna, Alhaji Abdulaziz Yari, da ‘yan majalisar tarayya da masu rike da madafun iko daga jihar da kuma wadansu manyan ‘yan siyasa na jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back To Top