Ni ce mace tilo ‘yar-takarar majalisar tarayya a Kano –Ummul-Khairi BB Faruq

Barista Amina Ummul-Khairi Ibrahim BB Faruk

Barista Amina Ummul-Khairi Ibrahim BB Faruk

Tura wannan Sakon

Daga Musa Diso

Wata fitacciyar Lauya kuma gogaggiyar ‘yar siyasa mai son ganin ci gaban al’umma musamman matasa maza da mata, Barista Amina Ummul-Khairi Ibrahim BB Faruk ta ce, ta fito neman takara na dan majalisar tarayya daga yankin karamar hukumar Gezawa da Gabasawa domin ci gaban al’umma da bunkasar tattalin arzikin kasa da kuma samar da zaman lafiya ga al’umma.

Ta ce, tabbas babu wata kasa a duniya da za ta ci gaba idan har al’umma suna cikin talauci da rashin ilimi da rashin aikin yi da kuma rashin tasro. Barista Amina Ummulkhairi ta yi jawabin a lokacin da take ganawa da manema labarai ciki har da wakilin jaridar Albishir a babban birnin Kano a makon da ya gabata .

Ta ce, babu shakka tun da daga 1999 zuwa 2023 babu wani abu da mazabar karamar hukumar Gezawa da Gabasawa ta samu daga wakilcin ta na tarayya wannan wani babban abin takaici, wannan ya faru ne saboda rashin gogewa da kuma rashin sanin makamar aiki.

Ta ce, yawancin ‘yan majalisar da suke wakiltar al’umma a majalisa kashi 80 da cikin 100 duk ‘yan dumama kujera ne, ba su san ma aikin su ba domin haka a matsayinta na gogaggiyar lauya wanda ta san dokoki na kasa da kuma hanyoyin da za`a bi a sama wa al’umma romon dimokaridiyya za ta iya kokarin ta wajen ganin jama`a sun yi na`am da wakilcinta. Umuml-khari ta ce, daya daga kalubalen da mazabar karamar hukumar Gezawa da Gabasawa ke fuskanta a yanzu haka shi ne, rashin samar da wani department ko college na jami`a a mazabar wanda zai saukaka wajen samar da ingantaccen ilimi na gaba da sikandire, babu shakka abin takaici ne da kuma uwa uba rashin masana`antu domin ci gaban matasa maza da mata.

Ta ce, rashin ilimi ya sanya mata daga Arewa koma baya wajen shiga harkokin siyasa sanin kowa ne cewa, ilimi yana da muhimmiyar rawa a rayuwar dan’adam domin ilimi shi ne ci gaban al’umma kuma Allah da kansa ya ce, a nemi ilimi a ko’ina yake domin shi ne garkuwar al’umma kuma zan yi iya kokarina naga cewa, mazabar da nake wakilta ba`a barta a baya ba wajen samar da harkar ilimi musamman ilimin gaba da sikandire da kuma na yaki da jahilci.

Ummul-khairi ta bayyan cewa, tun daga zamanin Annabi Adam zuwa yanzu ake haihuwa amma abin takaicin anan shi ne idan mace taje haihuwa a wannan mazabar saboda babu asibiti na musamman sai kaji anc e ta mutu, sannan kuma ba za mu yarda da wani bako ya ya zo ya ce, zai mana constituency project ba dole sai da hadin kan stakeholders kuma ni a matsayina na wakiliya bazan zartar da wani abuba sai na nemi yardarm al’ummar mazaba ta domin jama`a nake wakilta kuma su suka zabe ni, domin haka ba zan gudanar da wani abu ba sai da yardar su.

Ta ce, yunwa da talauci da rashin aiki yi ya fi kowace irin AK47 illa a duniya kuma da gangan aka bar mutane cikin jahilci domin shi jahili ba shi da wata kyakkyawar makoma domin haka a matsayina na ‘yar takarar neman majalisar tarayya idan har aka zabe ni zan inganta rayuwar al’umma domin wannan shi zai kawo ci gaba da kuma zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Daga karshe, ta bayyan gwamnatin APC a karkashin shugabancin Muhammad Buhari da cewa, ta gaza kuma duk alkawarin da ta dauka na harkar tsaro da cin hanci da rashawa babu daya daga ciki da ta cika alkawarin, domin haka jama`a su zabi cancanta da kuma inganci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *