Nijeriya a yau, ta fi ta jiya armashi -Fadar shugaban kasa

Daga Abbas Yakubu Yaura
Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa, N-jeriya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fi armashi a yanzu fiye da lokacin da ya hau mulki a shekarar 2015.
A martanin da ta mayar ga ra’ayin edita da jaridar Daily Trust ta buga, fadar shugaban kasar ta bayyana buga labarin cewa, ba ta da masaniya. Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce marubutan sun yi daidai cewa Nijeriya kamar kowace kasa a duniya tana cikin mawuyacin hali.
A cewarsa, “duk wani batu cewa, gwamnatin Buhari ba ta bar Nijeriya a wuri mai kyau kamar yadda muka same ta ba – musamman kan muhimman ginshikan tattalin arziki, tsaro da cin hanci da rashawa, hasashe ne tsantsa.
“Gaskiya ba ta neman ado, domin a bangaren tsaro kuwa, a baya-bayan nan a shekarar 2015 kungiyar Boko Haram ta mamaye yankin da ya kai girman kasar Belgium a Nijeriya. A yau, ba su da wani yanki na Nijeriya da za su yi magana.
A cikin watan Maris, sojojinmu sun kawar da shugaban ISWAP a wani hari ta sama da leken asirin Birtaniyya – shaida ga sabuwar amanar da abokanmu ke da ita a gwamnatinmu, ba gwamnatocin da suka gabata ba.
“Har ila yau, gwamnatinmu ita ce kadai a tarihin Nijeriya wajen aiwatar da hanyoyin magance rikicin makiyaya da manoma ta hanyar babban tsarin mu na kawo sauyi na kiwo na kasa, tuni aka kafa wuraren kiwo a karkashin shirin. “Saboda haka ba daidai ba ne a ce babu abin da aka tabuka,” in ji shi.
Ya ce, “Shekaru bakwai lokaci ne mai tsawo kuma sabbin manajojin nasu na iya zama ba su san cewa a shekarar 2015 Nijeriya a yau, ta fi ta jiya armashi -Fadar shugaban kasa suna bukatar shingaye a wurarensu da kuma manyan jami’an tsaro – kamar yadda sauran manyan cibiyoyi masu muhimmanci suke yi.
Ya ce, sun cire duk wadannan abubuwan, hakan ya nuna karara cewa, barazanar da ake yi, kamar yadda suke a wancan lokacin ta ragu. A kan cin hanci da rashawa kuwa, ya ce, gwamnati ta ga an dawo da daruruwan miliyoyin kudaden da aka sace daga kasashen waje aka yi amfani da su a matsayin kudaden jin dadin jama’a da aka rarraba kai tsaye ga marasa galihu a lokacin annobar korona da kuma samar da ababen more rayuwa da aka dade ana yi- tituna da gadoji d jirgin kasa da kuma sha’anin mulki, a cewarsa.
Wannan ya samo asali ne kai tsaye sakamakon tsare-tsare da gwamnatin Buhari ta yi kamar manufofinmu na tona asirin wanda ke bai wa ‘yan Nijeriya kwarin gwiwar bayar da rahoton cin hanci da rashawa ba tare da tsoro ba.
“Bugu da kari, hakan ya sake nuna sabon amincewar abokan huldarmu na duniya, sakamakon kokarin gwamnatinmu. Wadannan abokan hadin gwiwar sun ki mayar da kudaden sata ga gwamnatocin da suka gabata shekaru da yawa, suna sane da cewa, za a sake sace su.
“Abin da ya fi muhimmanci, abin da gwamnatin Buhari ta yi wajen samar da hanyoyin da za a bi domin hana cin hanci da rashawa da suka hada da karfafa ofishin babban mai binciken kudi da inganta karfin hukumomin yaki da cin hanci da rashawa ta hanyar sanya hannu kan wadansu dokoki da kuma umarnin zartarwa; aiwatar da asusun baidaya (TSA), mai ba da labari; aiwatar da tsarin kula da kashe kudi na jama’a da tsarin kula da lissafin kudi da dai sauransu.
Ya kuma bayyana cewa, shirin shugaban kasar ya bai wa al’ummar kasar kwarin gwiwar hana shigo da shinkafa daga kasashen waje, inda ya ceto dala miliyan 5 a kullum a kasuwar musayar kudi, ya ce “Mun ga dalar shinkafa a jihohi da dama da suka hada da Kebbi da babban birnin tarayya da Neja da Gombe da kuma abin mamaki jihar Ekiti.
Ya bayyana cewa, kasar ta shaida yadda aka kafa hadaddun kamfanonin shinkafa guda 54, da kananan masakun shinkafa 1,000, da kuma takin zamani 57 da aka farfado da su ko kuma aka sake gina su domin bunkasa noman. “A yau jihar Nasarawa tana fafatawa da Neja a harkar noman sukari kuma jihar Kaduna na gab da fara aikin masana’antar sarrafa karfe.
Tattalin arzikin mai aiki ne kawai zai iya ba da wadannan. Daya daga cikin manyan kura-kurai da masu adawa da shugaba Buhari suke yi, shi ne yarda da tunaninsu da farfagandar da suka yi a kan salon siyasar da suka yi imani da shi. “Ga wannan shugaban kasa, daya daga cikin manyan jarin da gwamnati mai ma’ana za ta iya yi shi ne, inganta rayuwar wadanda ke kan mataki mafi karanci na zamantakewa. Wannan gwamnatin tana da fiye da mutane miliyan 20 da ke cin gajiyar canjin kudi na sharadi da ciyar da makarantu da sauran saka hannun jari na zamantakewa, shirye-shiryen SIP.
“A lokacin da duniya ke cikin wahala, muna fuskantar kalubale ba tare da kirkiro su a inda babu. Ba riya ba ce cewa, babu nasarori a inda suke ba ya taimaka wa kowa. A maimakon haka, bari mu mai da hankali ga abin da muka cim ma domin mu ci gaba da ginawa a kan nasarorin domin magance sababbin kalubale da ke ci gaba da tasowa.