Nijeriya ta karbi riga-kafin korona

Najeriya na sa ran samun riga-kafin cutar korona nan da Karshen watan Janairu yayin da take kokarin kare kashi 40 cikin 100 na al’ummarta daga cutar a wannan shekarar da kuma kashi 30 a shekara mai zuwa.
Zubin farko zai kunshi allurar guda 100,000 ta Pfizer-BioNTech, wadda wani shirin Majalisar dinkin Duniya zai samar mai suna korona.
Da farko kasar za ta fara yi wa ma’aikatan lafiya riga-kafin da masu kai agajin gaggawa da shugabanni da mutanen da ke da wasu cutuka da kuma tsofaffi, a cewar shugaban hukumar lafiya a matakin farko, Faisal Shuaib. Kasar na fatan samun guda miliyan 42 da za ta ishi daya bisa biyar na jama’arta, a cewarsa.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta kaddamar da shirin Cobad ne domin taimaka wa kasashe marasa karfi saboda fargabar kasashe masu arziki za su wawashe ta.
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya fada a makon da ya gabata cewa kasarsa za ta karbi riga-kafin ta shirin Cobad nan da tsakiyar 2021 bayan ta fara biyan miliyan 283 na kudin kasar (dala miliyan 19).
Mutanen da suka harbu da cutar korona a Najeriya sun kai 92,705 sannan an sallami mutum 76,396 daga asibiti bayan an tabbatar sun warke, yayin da 1,319 suka mutu tun bayan bullar cutar a kasar.