Nijeriya ta tsaurara tsaro a asibitoci, makarantu -Sufeton ‘yan-sanda Alkali

Babban Sifeton ‘yan sandan Nijeriya Usman Alkali
Daga Mahmuda Gambo Sani
Sufeton ‘yan-sandan Nijeriya Usman Baba Alkali ya umarci kwamishinonin ‘yan-sandan jihohi 36 da babban birni Abuja, su kara tsaurara matakan tsaro a asibitoci da kuma kare jami’an kiwon lafiya.
A cikin sanarwar da kakakin rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ta ce, Baba ya bayar da umarnin ne a lokacin da yake bitar rahotannin al’amuran tsaro daga sassan kasar.
Ya ce, kwamishinonin rundunar a matakin jihohi su tabbatar da tsaro a makarantu da sauran gine-ginen gwamnati. Shugaban ‘yan-sandan ya umarci kwamishinoninsa da su tabbatar da cewa, ana gudanar da sintiri a-kai-a-kai da bincike da kai samame domin dakile ayyukan ‘yanta’adda da ake aikatawa a jihohin kasar.
Ya ce, manyan jami’an rundunar a matakai daban-daban da su bayar da fifiko wajen amfani da hanyoyin tattara bayanan sirri wajen gano maboyar miyagu tun kafin su kai hare-harensu.
Nijeriya dai na daya daga cikin kasashen yammacin Afirka da ke fama da matsalolin tsaro, musamman hare-hare a makarantu da asibitoci da sauran wuraren da jama’a suke taruwa.