Nijeriya za ta kuma fuskantar ambaliya a sassanta -NIMET, NIHSA

Ambaliya: Zangon Kabo ya jajanta wa ‘yan-kasuwar Kwari

Ambaliya a kabo

Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani

Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya NIMET da takwararta ta NIHSA da ke hasashen zubar ruwan sama, sun yi gargadi kan yiwuwar fuskantar matsananciyar ambaliyar ruwa a jihohin shiyyar Arewa ta tsakiya da kudu maso yammacin kasar.

Darakta Janar na hukumar NIMET, Farfesa Mansur Bako Matazu ya ce, hasashensu ya nuna yiwuwar samun mamakon ruwan sama a yankunan 2 wanda zai zama kari kan ballewar wadansu madatsun ruwan kasar.

Hasashen hukumomin biyu na zuwa ne a dai dai lokacin da jihohin Binuwai da Kogi ke tsaka da fuskantar mummunar ambaliyar ruwan da ta haddasa asarar rayukan jama’a da kuma dimbin dukiya, ambaliyar da bayanai ke cewa, ita ce mafi muni da kasar ta gani tun bayan makamanciyarta a shekarar 2012.

Farfesa Matazu ya ce, tun a watan Fabrairun da ya gabata suka yi hasashen samun ambaliyar ruwa a sassan kasar, sannan kuma suna tunatar da al’umma halin da ake ciki a sanarwar hasashen yanayin da suke fitarwa a kowanne wata. Farfesa Matazu ya ce, a shekaru masu zuwa za a samu ruwan sama mai yawan gaske, wanda hakan ke cikin matsalolin sauyin yanayin da aka fuskanta.

A daminar bana dai, jihohin Nijeriya 29 daga cikin 36 da kasar ke da su ne suka fuskanci ambaliyar ruwa, wadda kuma ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da lalata dukiyar miliyoyin Naira musamman a jihohin arewacin kasar da suka kunshi Taraba da Jigawa da Kogi da kuma jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *