NLC ta yi watsi da tsarin ‘‘ba aiki ba biya’’

Kungiyar kwadago ta NLC ta yi wancakali da tsarin gwamnati na ‘’ba aiki ba biya’’ da take son yin amfani da shi kan Malaman jami’o’i da suka shafe watanni 8 suna yajin aiki.
NLC ta bukaci gwamnati da ta cika dukkanin alkawuran da ta kulla da kungiyar ASUU gabanin komawa yajin aikin, ciki har da abin da ya shafi hakkokinsu na albashi da kuma kyautata aikinsu.
taro da kwamitin kolin kungiyar ya bayar, bayan ganawarsu a jihar Kebbi xauke da sa hannun Ayuba Wabba ta bayyana cewa, wajibi gwamnati ta saki hakkokin malaman kungiyar ASUU a tsawon lokacin da suka xauka suna yajin aikin.
An shafe tsawon watanni 8 ana kai ruwa rana tsakanin gwamnati da kungiyar ASUU dangane da yajin aikin gabanin cim ma jituwa a kwanan nan, wanda ya bayar da damar janye yajin aiki.
Sai dai Ministan kwadago, Mista Chris Ngige ya ce, har sai kotu ta kammala shari’ar da ke gabanta game da yajin aikin tukuna za su samu tabbacin yiwuwar biyan malaman ko akasin haka.