NNPP ta shirya korar gwamnatin APC a Gombe -Auwalu Seiko

Auwalu Seiko

Tura wannan Sakon

Danjuma Labiru Bolari, Daga Gombe

A lokacin da guguwar siyasa ke ta kara kadawa, ana shirin fuskantar babban zaben gama-gari na shekarar 2023, Auwal Isiyaku Seiko, ya ce, domin al’umma sun gaji da mulkin kama-karya da rashin taimako.

Auwal Seiko, da jam’iyyar ta bai wa takarar dan majalisar dokokin jiha a Gombe ta Arewa ya ce, jam’iyyar saboda yadda take da manufa mai kyau, ya sa kowa yake ta kokarin ganin ya shiga domin ceto kasar nan daga halin da take ciki na tsadar rayuwa da rashin aikin yi.

Ya kara da cewa, tun daga matakin tarayya har zuwa kan jihohi, jam’iyyar NNPP habaka take yi tana janye sanatoci da jiga-jigan ‘yan siyasa suna barin jam’iyyunsu suna komawa jam’iyyar NNPP, inda ya tabbatar da cewa, a shekarar 2023 jam’iyyar za ta iya kafa gwamnati a cikin sauki.

Ya yi alkawarin cewa, “Idan aka zabe ni a matsayin dan majalisar jiha a Gombe ta Arewa, sai na kawo canjin da ba a taba yi ba, kasancewata wakilin Inyamurai a kasuwar hatsi, zan hada kai da su wajen ganin mun taimaki matasanmu da kuma kawo mana wasu abubuwan ci gaba a dalili na.”

A cewarsa, duk wata alama ta faduwar zabe a jam’iyyar APC ta cika, da an je ranar zabe kawai jam’iyyar NNPP za a zaba tun daga kan gwamna zuwa ‘yan majalisu, saboda jam’iyyar APC an gaji da ita, domin ita ta kawo duk wata tsadar rayuwa.

Ya kara da cewa, saboda yadda jam’iyyar ta karbu yasa Peter Obi ya amince zai bar jam’iyyarsa ta Labour Party ya dawo ya hade da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, don zamar masa mataimakin shugaban kasa a 2023.

Daga nan sai ya yi kira ga matasa da mata da ba su da katin zabe da su gaggauta su mallaki katin zabe, domin sai da katin za a yaki annobar APC a kore ta a mulki, a kafa shugabancin jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *