NNPP za ta bayar da mamaki a zaben 2023 – Gayawa

Daga Musa Diso
Wani dan kasuwa kuma mai sana’ar siyar da kaji a kasuwar Muhammad Abubakar Rimi da ke Sabon Gari Kano, Alhaji Sani Musa Gayawa ya ce, jam’iyyar NNPP za ta bayar da mamaki a zaben 2023.
Ya ce, tabbas ganin yadda ‘yan Nijeriya suke tururuwa da dafifi da kuma nuna goyon baya ga jagoran Kwankwasiyya duk lokacin da ya kai ziyara jahohi a kasar nan wannan ya nuna a fili cewa, al’umma sun gaji suna bukatar canji domin haka jam’iyar NNPP za ta lashe zaben 2023 a kasar nan.
Gayawa ya yi furucin a lokain da yake zantawa da wakilin jaridar Albishir a ofishinsa da ke kasuwar Muhammad Abubakar Rimi Sabon Gari Kano makon da ya gabata.
Ya ce, ‘yan Nijeriya a yanzu haka sun gaji da shugabanci jam’iyyar APC karkashin shugaban kasa Muhammad Buhari saboda rashin tsaro da talauci da hauhawar farashi na kayayyakin masarufi da kuma tsadar rayuwa da uwa uba rashin aikin yi ga matasa maza da mata. Sani ya kara da cewa, tun da aka kafa mulkin dimukaradiyya ba’a taba samun gwamnatin data gallazawa ya Nijeriya kuma ta addabesu domin a zamanin gwamnatin Buhari Nijeriya ta tsaya cik babu ci gaba babuharkar kasuwanci babu wani abin a zo a gani da dan’adam zai ce san barka tabbas wannan wani babban kalubale ga ‘yan Nijeriya.
Ya ce, maganin wannan kasa a yanzu shi ne samar da shugaba jajirtacce, tsayayye mai hangen nesa, mai kishin al’umma da kuma ganin Nijeriya ta ci gaba da kuma dawo da martabarta a matsayin uwa a Afirka domin haka jagoran Kwankwasiyya shi ne mafita in ji Gayawa.
Daga karshe, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su fito kwansu da kwarkwatarsu ranar zabe da su zabi cancanta da kuma jam’iyyar NNPP domin ita ce kawai za ta fitar da aya daga rogo.