NNPP za ta warware matsalolin Nijeriya -Sarkin dillalai

Tura wannan Sakon

Isa A. Adamu Daga Zariya

An bayyana jam’iyyar NNPP da cewar ita ce za ta kawo karshen matsalolin da suke addabar Nijeriya, musamman matsalolin tsaro da ke addabar Arewa da kuma kasa baki daya. Bayanin haka ya fito ne daga bakin Sarkin Dillalan Tudun Wadan Zariya Alhaji Ahmed Shehu, lokacin da ya amsa tambayoyin wakilinmu da ke Zariya, kan zaben shekara ta 2023 in mai duka ya kai mu.

Alhaji Ahmed Shehu wanda kuma ke kasancewa mai neman takaerar majalisar jihar Kaduna a mazabar Zariya – kewaye a karkashin jam’iyyar NNPP, a zaben shekara ta 2023, ya nunar da cewar, babu ko shakka, in an dubi wadanda ke cikin jam’iyyar NNPP, za a fahimci cewar, mutane ne da babu abin da ke gabansu, sai me a su yi domin tallafa wa al’umma da kuma ayyukan da za su aiwatar domin al’umma su yi murna da zaben da suka yi ma su, ba al’umma su y da – na – sani – ba.

Ya bayar da misali da jagoran jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso na mukaman da ya rike a baya na gwamnan jihar Kano na ayyukan ci gaban al’umma da ya aiwatar da kuma yadda ya bar ayyukan da suka zama abin koyi ga gwamnoni da dama da suke arewa da kuma Nijeriya baki daya. Alhaji Ahmed Sarkin Diilalan Tudun Wada ya kuma bayyana cewar, baya ga Injiniya Kwankwaso a kwai fitattun al’umma da babu abin da ke zukatansu sai halin da Nijeriya da kuma ‘yan Nijeriya ke ciki, dukkansu.

A cewar Sarkin Dillalai, sun shiga jam’iyyar NNPP ne, domin su hada hannu da Kwankwaso a kawo karshen matsalolin da suke addabar ‘YAN Nijeriya a wannan lokaci. Sarkin Diilai ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya, musamman wadanda suka isa jefa kuri’a da su sa kishin Nijeriya da kuma kaucewa siyasar kudi da son rai, wanda a cewarsa, shi ya jefa ‘yan Nijeiya a halin tsadar rayuwa da ake ciki, kama da rashin – tsaro da kuma sauran matsaloli da ba za su kidayu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back To Top