Nusarwa kan tushen kafuwar birnin Kano

Tura wannan Sakon

Daga Hauwa Hamza

Idan muka duba tarihin Kano, muka cire labarin Dala da barbushe, da gunkinsu tsunburbura, za mu ga cewa, mulki a Kano ya fara ne da zuwan mafarauta, daga kauyen Gaya. A wancan lokacin, dagatan wadannan garuruwa zaman kansu suke yi.

Ba ruwansu da kowa, su wadannan ‘yan farauta, da suka zo nan garin, sai suka yi sansani a Madatai, karkashin shugabanninsu irin su, Gwale da Guguwa wadanda su ne manyan maguzawa.

Bayan farautarsu ta yi matukar Nasara har jama’a masu yawa suka taru a wurin don su ci albarka, inda suka koma noma saboda samun kwadago cikin mutanen gari, da kuma iyalinsu.

Bayan sun yi noman da yawa, sai yunwa ta afku a kasashen Afirka ta yamma, ba a sami abinci  a ko’ina ba, sai an zo nan Kano, a saboda haka wadannan ‘yan farauta da suka yi noma suka zama manyan attajirai, suka yi arziki, musamman na bayi da kuma dawakai da sauran kayan alatu.

Kabilu iri-iri suka zo Kano domin su kubuta daga yunwa. Wadannan kabilu su  ne, Barnawa, Katsinawa, Daurawa, Zamfarawa, Gobirawa, Kambawa, Adarawa, Azbinawa da sauransu. Daga nan ne kuma jama’a daban-daban suka fara kafa kauyuka, suna nada dagatansu.

Wadannan kauyuka na farko su  ne, Lambu, Kanwa, Kwankwaso, Tamburawa, Yankatsari, Mariri, Gunduduwa  da sauransu.

Da jama’a suka yi yawa, sai kauyukan Kano suka kai har sugugum, to, a nan ne fa tun da babu wani Sarki sai dai dagatai, kuma ga mutane sun yi arziki, wasu wadanda suke bin Daura a wancan lokacin suka dinga kawo wa Kano hari, suna kame Kanawa.

Da wannan abu ya dami jama’a, sai suka kai kara wajen Sarauniyar Daura, ta waccan lokaci, suka nemi  da  ta  nada masu sarki, wanda zai kare su, sai ta nada masu Bagauda ya zama sarkin Kano na farko.

Tun da aka nada Bagauda sarkin Kano, tun sannan kuma duk dagatain kauye suka zama wakilan sarki, a kauyukansu. Idan sarki ya nada wani a cikinsu, sai ya yi hannu da shi, bisa amincewarsa da amanarsa. Zai rike wa sarki wannan mukami, tun daga ranar da aka nada shi. Wannan al’ada ta ci gaba har ta bunkasa, dagatai kuma suka rinka samun umarni daga sarki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *