NYSC ta ki amincewa da cibiyoyin ilimi 8- Daga kasashen Benin,Kamaru da Nijar

Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani

Hukumar Kula da masu yi wa kasa hidima (NYSC) ta fitar da jerin sunayen cibiyoyin karatu da ba za a yi wa wadanda suka kammala karatunsu rajista ba a lokacin kwas din yi wa kasa hidima na wannan shekarar.

Majiyar jaridar ALBISHIR ta rawaito cewa, cibiyoyin da abin ya shafa sun fito ne daga kasashe 3 wadanda suka hada da Benin da Niger da kuma Jamhuriyar Kamaru.

Wata sanarwa mai dauke da kwanan watan 5 ga Maris, wacce aka aike wa Ko’odinotoci masu Kula da Jihohi da na babban birnin Tarayya ta lissafa cibiyoyin karatun na kasashen waje 8 da suka hada da, Jami’ar Al-Nahda dake Jamhuriyar Niger

Sauran cibiyoyin da ke Jamhuriyar Benin su ne, Ecole Superieur Sainte Felicite da Ecole Superieur D Adminstartion et DEconomie da Ecole Superieur DEnseignement Professionalelle Le Berger (ESEP La Berger) da kuma Ecole Superieur St. Louis D. Afrique.

Sauran su ne Superieur de Comm. Dord Et de Management (ISCOM) Jamhuriyar Benin, da kuma Institut Superieur de Formation Professionelle (ISFOP) da Jami’ar Bamenda, da ke Kamaru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *