Osinbajo ya cancanci zama shugaban Nijeriya -Kwamred Igwe

Osinbajo ya cancanci zama shugaban Nijeriya -Kwamred Igwe

Prof. Yemi Osinbajo

Tura wannan Sakon

Daga Rabiu Sunusi

An buKaci jama’ar Kasar nan da su maida hankali wajen zaBen mataimakin shugaban Kasa, Fafesa Yemi Osinbajo a matsayin shugaban Kasar Nijeriya a shekarar 2023. Hakan na fitowane daga bakin shugaban haDaDDiyar Kungiyar matasan Nijeriya ta Coalition oF Bibrant Youths ActiBies, Kwamred Muhammad Abdullahi Abubukar da aka fi sani da (IGWE) a wata hira da Albishir da ya yi.

Igwe ya ce, a wannan gabar da ake ciki halin yanzu babu wanda ya dace da zama sabon angwan Kasar nan kamar mataimakin shugaban Kasa Osinbajo. Haka kuma ya tabbatar da cewa, kasancewarsa mutumin da shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kan bar masa jagorancin Kasa, kuma ya tafiyar da ita ba tare da wata matsala ba.

Ya ce, lallai shi mataimakin shugaban Kasa, Osinbajo mutum ne da bai da nuna Bangaranci da bambancin addini a ko wariya ga wata ko waDansu Kabilu ko sashe Hakan ma ya ce, su a shirye suke kan batun dukkan wani Kalubale da za su tunkara musamman ga waDanda za su ga sun Dauko wani Dan takara da suke da ra’ayi kuma ba addininsu balle Kabila daban da na su saBanin ‘yan takarar mu na arewa.

Ya kuma Kara da cewa, duba da yadda ake ciki da halin da ake ciki yanzu babu wanda Kasar take buKata kamar shi a halin yanzu. Shugaban Kungiyar ya yaba da irin yadda ya karbu ga jama’ar ta yadda halinsa ba wani abin Ki ba ne.

Haka zalika ya Kara buKatar al’ummar Kasar Nijeriya da su Kara nazari da tunani kan zaBar Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin shugaban Kasar Nijeriya da kai ga cim ma kyakkyawan niyya da yake da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *