PDP ta fi cancanta ta kafa gwamanti a Jigawa -In ji Adamu Alhassan

Mustapha Sule Lamido
Alhussain daga Kano
Dan takarar jam’iyyar PDP, Alhaji Mustapha Sule Lamido, ya fi cancanta ya zama gwamnan jihar a zaben 2023 , ganin yadda yake da kyakkyawar mu’amala ga al’ummar jihar daman a sauran jihohi.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin wani masoyin sa dake zaune a jihar Kano Alhaji Adamu Alhassan Muhammad, a lokacin da yake nuna farin cikinsa a kan nasaraR da Mustapha Sule Lamido ya samu na zaBen fitar da gwani.
Alhaji Adamu Alhassan Muhammad, ya ce, babu shakka nasar abin farin ciki ne ga duk wani dan’jam’iyyar PDP da ke jihar Jigawa dama daukacin al’ummar jihar, za mu ci gaba da ba shi hadin kai da goyon baya domin ganin ya samu hayewa a zaben 2023, a wani bincike da suka gudanar sun nuna cewa, hatta sauran wadansu ‘yan jam’iyyun za su kada wa Mustapha Sule Lamido kuri’unsu.
Matukar ya samu nasara zai habaka tattalin arzikin jihar ta fannoni da dama a matsayin sa wanda ya san harkokin kasuwanci, sannan kuma zai tafiya da matasa musamman tura su karo karatu da kafa wurarin koyar da sana’oin dogaro da kai.
Kan damar da PDP ta samu a jihar sai ya yi kira ga al’ummar ta jihar musamman ‘yan PDP su tabbatar sun karbi katin zabe su zabe PDP.
Canza APC a jihar da sabuwar jam’iyyar NNPP ba wani abu ba ne da yardar Allah abin kawai da ake jira shi ne lokaci, saboda haka ba sa ba mu tsoro.
Daya juya kan nasarar Alhaji Atiku Abubakar ya ce, idan ya zama shugaban kasa zai dawo da martabar tattalin arzikin Nijeriya da yanzu haka ya shi ga wani hali na rashin tabbas.
Daga karshe, ya yi kira ga ‘yan PDP na jihar Jigawa da kasa baki daya da su hada kansu wanda kuma aka bata ma saya yi hakuri.