PDP Ta Yi Na’am Da Na’urar Tantance Masu Zabe – Wusono

Tura wannan Sakon

Daga Isa A. Adamu, Zariya

Jam’iyyar PDP na goyon bayan hukumar zabe mai zaman Kanta ta Nijeriya [INEC] na amfani da na’urar tantance ma su zabe, kafin su yi zabe, a zaben shekara ta 2023.

Sakataren jam’iyyar PDP a jihar Kaduna, Alhaji Ibrahim Aliyu Wusono ya bayyana kalaman da suka gabata, a lokacin da wakilinmu ya ji ta bakinsa kan wannan na’ura da hukumar zabe mai zaman kanta ta fara amfani da na’urar a zaben gwamna da ya gudana a jihar Osun.

 Alhaji Ibrahim Wusono ya ci gaba da cewar, zaben jihar Osun, zaben da al’umma uka yi shi aka ba su, a alilin amfani da wannan na’ura da ta kare duk wata hanya da za a sa son rai ko kuma a canza alkaluman zaben da al’umma suka yi.

Sai dai kuma Alhaji Wusono ya nunar da cewar, bayan kammala zaben, da aka yi da wannan na’urar, a cewarsa, wasu da suka nuna rashin goyon bayansu da sakamakon da aka samu, wanda har sun motsa, domin nuna bukatar hukumar zabe ta canza alkalummar zaben da aka samu a karshen zaben, domin, a cewarsa, su na da uwa a kusa da murhu.

Alhaji Ibrahim Wusono ya bayyana matukar jin dadinsa da mahukumtan hukumar zabe suka fahimci, yin zabe a cikin adalci da kuma bayyana sakamakon zaben bisa yadda aka gudanar da zaben, zai kara wa hukumar zabe mutunci a idon al’umma, musamman wadanda ke furta cewar, ko da sun yi zaben, ba za a ba su abin da suka zaba ba.

Kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta a Nijeriya ta ce, a cewar Alhaji Wusono, an kawo wannan na’urar ce domin a gyara kura – kuran da ake samu a lokutan zabubbuka, sakamakon da aka samu, zai sa al’ummomin Nijeriya su yadda hukumar zabe da gaske ta ke I, na gudanar da zabubbukan shekara ta 2023 a cikin bin doka da adalcin bayyana sakamakon zaben da al’umma suka yi ba tare da an canza sakamakon ba.

In ba a mantaba, a cewar Alhaji Aliyu Wusono, domin a kawo karshen wasu matsalolin zabe ne da hukumar zabe mai zaman kanta [ INEC] a shekara ta 2015 da 2019 aka yi amfani da na’urar da ake kira [ CARD READER], ta yi amfani da wannan na’urar, suka gano wasu matsaloli, wanda kuma, a shekara mai zuwa wannan hukuma, kamar yadda Alhaji Wusono ya ce, ta sa ke samar da wata na’urar da za ta tantance duk wani mai zabe, da kuma kare faruwar ma su kada kuri’a sau biyu ko ma fiye da hakan a shekara ta 2023, a cewarsa, bayan ta gwada wannan na’ura a zakben jihar Osun da ya gabata.

A game da rage matsalolin da ake samu a lokutan zabubbuka kuwa, sakataren jam’iyyar PDP a jihar Kaduna ya tabbatar da cewar, sabuwar na’urar, za ta rage matsalolin satar akwatin zabe ko kuma satar katin da ake dangwala zabe, duk kamar yadda ya ce, an yi maganin wadannan matsaloli da aka ambata.

A karshe, Ahaji Ibrahim Aliyu Wusono, ya yi kira ga jami’an tsaro da za su sa ido a lokutan zabubbuka, na kamar yadda hukumar zabe ta inganta ayyukanta domin ‘yan Nijeriya su gudanar da zabubbuka bisa kyakkywar tsari, su ma, a cewarsa, su sa idon ganin wasu matsaloli ba su kunno kai ba a lokutan zabubbukan shekara ta 2023, domin ‘yan Nijeriya su ga amfanin sabon na’urar tantance ma su kada kuri’a da za a yi amfani da shi, a zaben shekara ta 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *