PDP za ta lashe zabe 2023 – Awilo

Daga Musa Diso
Dan takarar neman kujerar majalisar jihar Kano a karkashin jamiyar PDP da ke karamar hukumar Gwale, Abdulhadi Dalhatu Awilo ya bayyana cewa, PDP za ta lashe zabe a 2023.
Ya ce, idan ka duba irin rayuwar da al’umma suke ciki a yanzu a karkashin jam
iyar APC da kuma jagoancin shugaban kasa Muhammad Buhari wanda ya haifar da matsaloli daban-daban na rashin aikin yi ga matasa maza da mata da sace-sacen mutane da kuma fatara babu shakka ya nuna cewa, babu wata mafita ga ‘yan Nijeriya illa su zabi jamiyar PDP a zaben 2023 domin kawo sauyi ga rayuwar al’umma.
Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan taron, kungiyar kakakin Dala a gidan Malam Aminu Kano dake Gwammaja.
Ya ce, jam
yar APC ta gaza kuma ta bada kunya domin ta kasa dorawa kan abun alheri da jamiyar PDP ta fara domin haka ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su zabi PDP, daga sama har kasa domin APC ba jam
iya ce ta ‘yan Najeriya ba, jamiya ce ta ‘yan jari hujja sun zo ne domin su debe kudin jama
a daga su sai yayansu domin haka ya kamata jama
a su yi alkalanci da kansu a tsakanin jamiyar APC da PDP wajen samar da zaman lafiya da ci gaban al’umma.
Daga karshe, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su zabi jam`iyar PDP domin itace mafita.