Pillars za ta biya tarar Naira miliyan 9 -Saboda cin zarafin Katsina United

Pillars za ta biya tarar Naira miliyan 9 -Saboda cin zarafin Katsina United

Pillars sun ci zarafin Katsina United

Tura wannan Sakon

Labari Salisu Baso

Hukumar shirya gasar Firimiya ta Najeriya, LMC, ta ci tarar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars naira miliyan 9 bayan saba ka’idojin da dokokin shirya gasar.

Za kuma a kwashewa Pillars din maki uku daga adadin makin da ta tara a kakar wasa bana.

Zalika idan ta sake aikata laifi a nan gaba, za a sake kwashe mata karin maki uku.

Wani karin matakin ladabtarwa da aka dauka kan kungiyar ta ‘Sai Masu Gida” shi ne, daga yanzu za ta rika buga wasannin ta na gida ne a filin wasa na MKO Abiola da ke Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya.

An kuma dakatar da filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata a Kano daga karbar bakuncin dukkanin wasannin gasar Firimiyar Najeriya har sai abinda hali ya yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *