PRP ta yi gangamin motsa jam’iyya -A Kano

Daga Abubakar Garba Isa
A makon da ya gabata jam’iyyar PRP ta yi taron shugabanninta na kananan hukumomi 44 da ‘yan takarorinta na jihar Kano.
A jawabinsa, dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar PRP, Salihu Tanko Yakasai ya tabbatar da kasancewarsa dan takarar gwamnan a PRP maganar janyewar takarata ba gaskiya ba ne.
Kuma maganar hadewa da wata jam’iyya ba gaskiya ba ne, muna tabbatar maku cewa, za mu yi takara kuma za mu ci zabe in Allah ya yarda.
A jawabinsa, dan takarar majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Birnin Kano, Alhaji Ibrahim Tahir ya yaba wa matasan jihar Kano da suke tururuwar shiga jam’iyyar PRP. Daga karshe, ya gode wa shugabancin jam’iyyar PRP a karkashin jagorancin shugabancin Alhaji Abba na Matazu.