PRP za ta tsayar da ‘yan takara a kowane mataki -Alkali Suhaibu

PRPLogo
Isa A. Adamu Daga Zariya
Yanzu haka jam’iyyar PRP a tarayyar Nijeriya ta kamala duk shirye – shiryen da suka dace, domin tsayar da ‘yan takara tun daga shugaban kasa ya zuwa gwamnoni da ‘yan majalisar jihohi da kuma na tarayya a zaben badi, wato shekara ta 2023.
Mataimakin shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PRP Alkali Su haibu Jafar Abubakar ya bayyana haka a zantawarsa da wakilinmu da ke Zariya, kan shirye – shiryen da jam’iyyar PRP keyi, domin tunkarar zaben shekara ta 2023 mai zuwa.
Alkali Suhaibu Jafar ya ci gaba da cewar, babbar matsalar da ke gabansu a halin yanzu ita ce, matsalolin shari’a da wadanda ke neman durkusar da jam’iyyar PRP A Nijeriya, amma duk da haka, a cewarsa, a kwai fitattun ‘yan takara da dama da suke son tsaya wa takara a jam’iyyar PRP da suke daukacin jihohin Nijeriya da Abuja da wasu ma, yanzu haka suna kasashen wajen, domin gudanar da wasu ayyuka, da suka shafi ciyar da jam’iyyar PRP gaba, musamman zaben shekara ta 2023.
Mataimakin shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PRP, Alhaji Suhaibu Jafar ya kara da cewar, yanzu abin da suke jira kawai shi ne a ‘yan kwanaki kadan, kotu za ta yanke hukumcin wannan shar’a, da wasu ke neman durkusar da jam’iyyar ba ciyar da jam’iyyar gaba ba, kuma da zarar an yanke hukumci, magoya bayan jam’iyyar da suke ciki da wajen Nijeriya, za su san halin da ake ciki.
Da kuma ya ke tsokaci kan ma su niyyar tsaya wa takara a zaben shekara ta 2023 kuwa, ya shawarce su da su ci gaba da yin duk shirye – shiryen da suka kamata, domin ganin jam’iyyar PRP ta lashe zabubbukan da za a yi a badi. A game da wadanda za su tsaya takara kuwa, Alkali Suhaibu Jafar Abubakar ya nunar da cewar, a kwai fitattun ‘yan siyasa da masana ilimi da suke tare da jam’iyyar PRP da suke koyarwa a jam’o’in Nijeriya da kuma sauran mutane daban – daban da suke da niyyar yin takara, kuma nan gaba kadan za su bayyana takarar da za su yi a zaben shekara ta 2023.
A game tsohon shugaban‘iyyar na kasa Farofesa Sule Bello da ya rasu kimanin wata takwas da suka gabata, Alkali Suhabu Jafar ya bayyana marigayin da cewar, a dan lokacin da ya jagoranci jam’iyyar PRP ya yi bakin kokarinsa wajen ganin jam’iyyar ta kafu a sassan Nijeriya ba arewacin Nijeriya kawai ba.
Ya kara da cewar, hatta wadanda ke hankoron su ne shugabanin jam’iyyar na kasa, kafin uban jam’iyyar ya rasu, ya rushes u, ya mika shugabancin jam’iyyar ga Farofesa Sule Bello da wasu ma su kishin jam’iyyar da suke sassan Nijeriya da kuma wasu da suke gudanar da harkokinsu a kasashen waje.
Alkali Suhaibu Jafar Abubakar ya kamala da kira ga dukkanin magoya bayan jam’iyyar PRP a Nijeriya, da su ci gaba da sauraron shugabannin jam’iyyar na halas da babu abin ke zukatansu, sai me za su yi, na ganin sun ciyar da jam’iyyar gaba, musamman a zabubbukan da hukumar zabe mai zaman kanta za ta jagoranta a badi, wato shekara ta 2023.