Rabon riga-kafin Korona : CISLAC, Transparency sun yi kiran a yi rabon adalci

Daga Mahmud Gambo Sani
Cibiyar bayar da Shawarwari kan mulki na gari wato The Civil Society Legislative Advocacy Centre (CISLAC) da kuma kungiyar kare hakkin dan adam ta (Transparency International Nigeria) sun yi kara ga mahukunta da su tabbatar da rabo na adalci da gaskiya yayin rabon allurar riga-kafin cutar Korona.
A jawabin da kungiyoyin suka fitar sun ce, sun yi farin cikin samun labarin cewa Nijeriya ta karɓi tallafin allurar riga-kafin Korona kusan miliyan 4 daga Jami’ar Oxford da kuma manyan kamfanonin harhada magunguna suka bayar.
Cibiyar ta CISLAC da Transparency son gode wa shirin (COVID-19 Vaccines Global Access Facility )(COVAX) wanda aka kirkira don tabbatar da samun damar yin allurar riga-kafi ga jkasashe matalauta da masu matsakaitan kudi.
Sun kuma yaba wa kungiyar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya bisa jagorantar wannan aiki, wanda zai tabbatar da cewa babu ƙasar da aka bari a baya wajen samun allurar.
Haka zalika, sun yi Kira ga hukumomi da su tabbatar da cewa aikin rarraba allurar rigakafin ya kasance a bayyane