Ramadan: Goman karshe na da mutukar muhimmanci, a dage -In ji Hamisu Aliyu

Ramadan: muhimmancin Goman karshe
Daga Alhussain Kano
Kwanakin da suka rage na watan Azumin Ramadan mai albarka babu shakka kwanakin ne masu matukar muhimmaci ga al’ummar musulmin Duniya, sabodahaka ya zama wajibi aka himma wajen neman kusanci ga Allah musamman karatun Alkur’ani da neman gafarar Allah da sauran ayyukan alheri.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin Alhaji Hamisu Aliyu Usman, a lokacin da yake tsokaci a kan kwanakin da suka rage na Ramdan.
Hamisu Aliyu Usman, ya ce, yana da kyau a yi amfani da kwanakin da suka rage masu albarka ci gaba da tallafa wa mara karfi musamman kai tallafi gidajen marayu. Ganin wata ne na amsar addu’a saboda haka ya zama wajibi a yi wa kasar nan addu’ar zaman lafiya domin a halin da ake ciki babu abin da take bukata irin addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali matukar aka koma ga Allah Allah zai kawo mana karshen halin da ake ciki na matsalr tsaro da sauran matsaloli.
A matsayinsa na dankasuwa ya yi ya nuna farin cikinsa a kan yadda ‘yankasuwa da sauran masu hali suke amfani da dukiyar su wajen taimaka wa marasa karfi a cikin watan na Ramadan yana fatan wannan kokarin da suka yi zai dore ko da bayan watan Ramadan ya wuce.
Ga masu rike da madafun ikon kasar nan kuwa sai Malamin ya tunatar da su cewa, su ji tsoron Allah da kuma rike amana su sani ranar gobe kiyama Allah zai tambaye su yadda suka tafiyar da mulkinsu. Daga karshe ya yi addu’ar ya ba mu alheran da ke cikin watan Ramadan ya karbi ibadu da aikin alhairin da ake gudanarwa a cikin watan ya sa a yi bukukkuwan karamar sallah lafiya.