Rana ba ta karya: Gobe APC za ta yi babban taro na kasa

Rana ba ta karya: Gobe APC za ta yi babban taro na kasa

Shugaban riko na APC Gwamna Buni

Tura wannan Sakon

Daga Mahmoud Gambo Sani

A gobe, jam’iyya mai mulkin Nijeriya, APC za ta gudanar da babban taronta na kasa, a babban filin taro na Eagle Skuare da ke Abuja.

Taron, wanda shugabancin riko na jam’iyyar a matakin kasa, a karkashin gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai-Mala Buni ya tsayar da ranar 26 ga Maris, 2022 domin gudanar da shi, inda za a zavi shugabanninta na kasa kan mukamai daban-daban.

Idan za a iya tunawa, tuni aka gudanar da makamancin taron, a matakan kananan hukumomi 774 da jihohi 36, da kuma babban birnin  tarayya, kuma tuni an kaddamar da su, kuma an ba su takardun shaidar tabbatar da su a kan mukaman nasu daban-daban.

Tun da farko, an sami rikice-rikice, a wadansu jihohin Nijeriya, kamar Kano da Sakkwato, inda daga bisani kotun tarayya ta warware rikicin, kafin a kai ga kaddamar da shugabancinsu.

Duk da cewa, akwai mabukata shugabancin jam’iyyar na kasa daga Arewaci, da kuma shiyyoyin Arewa uku, Arewa ta tsakiya, da Arewa maso gabas, da kuma Arewa maso yamma. Ana jin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi nune, wanda ya nuna kuwa shi ne, tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Adamu Abdullahi.

A shiyyar Arewa maso gabas, akwai Alhaji Ali Modu Sheriff, daga jihar Borno.

A yayin da a shiyyar Arewa maso yamma, akwai Alhaji Abdulaziz Abubakar Yari daga jihar Zamfara.

Wadanda ake jin za su gwada kwanji, akwai tsohon gwamnan jihar Binuwai, Sanata George Akume, da tsohon gwamnan Nasarawa, Sanata Tanko Al-Makura, da sauran makamantansu.

Za a iya cewa, ba a sam maci-tuwo ba, sai miya ta kare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *