Ranar hana shan taba ta Duniya 2023 : WHO ta yi bayani kan hadarin shan taba

Tura wannan Sakon

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Wani rahoto da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar ya bayyana cewa, Nijeriya na fuskantar mummunar illar cututtuka masu nasaba da hayaki inda aka yi asarar rayuka kimanin dubu 30 a shekarar 2022.

Wani daftarin rage cutar da taba sigari ta duniya ya nuna cewa, kimanin kashi 4.1 cikin 100 na manya a Nijeriya suna shan taba, wanda ke wakiltar kusan mutane miliyon 4.5 da kashi 7.9 cikin 100 maza ne, yayin da mata ke da kashi 0.3 cikin 100 na masu shan taba.

Da yake jawabi a bikin ranar masu shan taba ta duniya ta 2023, kakakin kungiyar Foundation for Consumer Freedom Adbancement (FCFA), Abisoye Micheal, ya ce, alkaluman na nuna bukatar gaggawa ga gwamnatin Nijeriya ta bayar da fifiko wajen samo dabarun rage cutar tabar sigari, kuma ya bukaci gwamnati ta dauki mataki irin wanda kasar Sweden ta dauka a baya. Ya bayyana cewa, ta hanyar yin amfani da tsarin kasar Sweden, Nijeriya za ta iya share fage ga sauran kasashen Afirika, ta yadda za ta bayar da misali wajen rage yawan shan taba da kuma samar da kyakkyawar makoma ga mashaya sigari da ma matasa da ke tafe.

Ya ce, gagarumar nasarar da kasar Sweden ta samu a bayyane yake yayin da take matsowa kusa da zama al’ummar da ba ta da hayaki. Ya kara da cewa, a cikin shekaru 15 da suka gabata, yawan shan taba a kasashen Turai ya ragu daga kashi 15 cikin 100 zuwa kashi 5.6 cikin 100 na ban mamaki, wanda ya mai da shi mafi karanci a duniya.

“Wannan nasarar ba wai kawai tana nuna raguwar shan taba ba, amma tana nuna raguwa mai yawa a cikin hadarin da taba sigari ke haifarwa ga kiwon lafiyar al’ummar kasa.

Har ila yau, hakan ya sanya kasar Sweden shekaru 17 a gaban burin da tarayyar Turai ke da shi kamar yadda Wannna kididdiga mai ban sha’awa, wadda shaida ce ga tasirin hanyar da kasar ta Sweden ta dauka na rage hadarin da ke tattare da taba sigari” a cewar Micheal. Ya kara da cewa, “habaka sigari da samar da sigari na kara tsananta karancin abinci mai gina jiki da rashin abincin ma kwacakwam, Noman taba yana lalata yanayin halittu, yana lalata kasa ta haihuwa, yana kuma gurbata ruwa da gurbata muhalli.

A cewar sa duk wata ribar da za a samu daga taba a matsayin amfanin gona na tsabar kudi ba za ta iya daidaita barnar da aka samu na samar da abinci mai dorewa ba a kasashe masu tasowa.” “Kusan mutane miliyan 828 na fuskantar yunwa a duniya.

Daga cikin wadannan, miliyan 278 (20%) suna Afirka. Bugu da kari, kashi 57.9% na mutane a Afirka na fama da matsananciyar karancin abinci.”

“Wannan yana kawo cikas ga nasarar da yankin ya samu na SDG 2 wanda ke Ranar hana shan taba ta Duniya 2023 : WHO ta yi bayani kan hadarin shan taba da nufin kawo karshen yunwa, samar da wadataccen abinci da ingantaccen abinci mai gina jiki, da inganta noma mai dorewa.”

Haka nan karfafawar manyan hanyoyin da ke haifar da karancin abinci da yanayin rashin abinci mai gina jiki na baya-bayan nan, kamar tashe-tashen hankula, matsanancin yanayi, da girgizar tattalin arzikin, yana kara hada wannan yanayin. Don haka, ayyukanmu na hadin gwiwa suna da mahimmanci, don haka kowa yana da damar samun isasshen abinci matukar an rage wannan annoba ta ta’ammali da taba Sigari a doron kasa.”

“Muna fuskantar babban kalubale wajen samar da abinci mai gina jiki sakamakon karuwar noman taba a yankin Afirka. Bayanai da ake samu sun nuna cewa, yayin da yankin da ake noman tabar ya ragu da kashi 15.7% a duniya, a Afirka ya karu da kashi 3.4% daga shekarar 2012 zuwa 2018.

A wannan lokacin, noman ganyen taba a duniya ya ragu da kashi 13.9%; duk da haka, ya karu da kashi 10.6% a Afirka. A cikin ‘yan shekarun nan, noman taba ya koma Afirka saboda yanayin da aka tsara wanda ya fi dacewa ga masana’antar taba, da kuma karuwar bukatar taba sigari”.

“WHO tana aiki tare da Mambobin Kasashe da sauran abokan hadin gwiwa don taimaka wa manoma wajen canjawa daga noman taba zuwa sauran amfanin gona a cikin shekaru biyu da suka gabata, wani shiri a Kasar Kenya ya taimaka wa manoman taba sigari sama da 2000 suka koma ga sauran amfanin gona, Wannan ya haifar da samun ingantaccen abinci mai gina jiki, karin samun kudin shiga ga manoma, ingantattun ayyukan noma da kuma gyara muhalli.

“Rahoton na nuna cewar an fara fadada wannan shiri zuwa kasashen Uganda da Zambia, kuma ya kamata a karfafa gwiwa ga dukkan kasashen Afirka dake noman tabar sigari”.

“Ya kamata gwamnatoci su tallafa wa manoman taba su canza zuwa wani nau’in amfanin gona ta hanyar kawo karshen tallafin noman tabar da kuma amfani da kudaden ajiya don shirye-shiryen maye gurbin amfanin gona don inganta abinci mai gina jiki wato ta hanyar Sauyawa daga taba zuwa kayan amfanin gona masu gina jiki don samun damar ciyar da miliyoyin iyalai da inganta rayuwar al’ummomi a Afirka”.

“Irin wadannan tsare-tsare kuma za su yaki kwararowar hamada da gurbacewar muhalli, da wayar da kan al’ummomin da ke noman taba sigari game da fa’idar ficewa daga shan taba ya zuwa noman amfanin gona mai dorewa da kuma fallasa kokarin da masana’antar taba ke yi na dakile ayyukan rayuwa mai dorewa a yankin Afirka”.

“Muna kuma kira ga kasashen da ke yankin Afirka masu arzikin taba sigari da su kara kaimi wajen aiwatar da sharuddan 17 da 18 na yarjejeniyar hana shan taba sigari ta(WHO FCTC) ta hanyar samar da doka da aiwatar da manufofi da dabaru masu dacewa, da ba da damar yanayin kasuwa ga manoman taba su koma gonakin noman abinci wanda zai wadata su da iyalansu don samun ingantacciyar rayuwa tare da inganta kare muhalli da lafiyar mutane.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *