Rarara, cin mutuncin ya isa haka

Rarara

Rarara

Tura wannan Sakon

Daga Kwamrade Ibrahim Abdu Zango

A wani lokaci kan nayi rubutu rangadede akan mawakin zamani Dauda Kahutu Rarara dan mutanen Katsina bisa ga niyya kyakkyawa. Ban sanshi ba, ban taba ganinsa ba, illa kawai kauna ta mutum da mutum.

Dauda Kahutu Rarara bakatsine ne, kuma watakil mazaunin Kano wanda ga almajiranci Allah Ya hore masa hikimar waka! Ban san ta yadda wannan fasaha ta samu ba, wanda cikin kankanin lokaci Dauda Kahutu Rarara wai har kyautar mota yakeyi da miliyoyin Naira! Dauda Kahutu Rarara ance yana kusa-kusa da Billa harma wai ya kusanci shugaban kasa Muhammadu Buhari, a kasancewarsa mawakin Shugaba Buhari da kuma cewa ya hito ne daga jihar Katsina, jihar Katsina itace jihar Shugaba Buhari, kuma shi wannan sabon mawaki wai sunan kauyensu Kahutu, watakila bangaren Daura yake ko kuma can hanyar Dandume Allah masani.

To Dauda Kahutu Rarara ya canza kalar wakarsa ta kasance ta cin mutuncin masu shi, abin mamaki kare da tallan tsire; Dauda Kahutu Rarara ya taba mutuncin wasu manyan ‘yan siyasar Kano; wato Maigirma Sardaunan Kano Malam Ibrahim Shekarau, tsohon Gwamnan Kano kuma mai mukamin sarauta a Kano kuma yanzu Sanata a tarayyar Nijeriya.

Yasa masa suna Duna, wato kare kenan ko? Haka ya kira tsohon Gwamna, kuma tsohon Sanata Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso Tsula wato Biri, haka yanzu kuma yake kiran Gwamna Ganduje da sunan Hankaka! To duk wannan ga alamu, ya gane cewa ‘yan siyasar Kano basa mutunta junansu har wani can daga jihar Katsina zaizo da kokon bara yake ciwa manyan Kano mutunci saboda rashin ta ido, domin Wallahi Tallahi Dauda Kahutu Rarara bana jin koda sau daya zai yiwa masari Gwamnan Katsina wannan cin kashin haka, kai bama Gwamna Masari ba, ko dan jagaliyar siyasar Katsina idan akwai Dauda Kahutu Rarara bai isa yayi masa cin fuskar da yake yiwa shugabanni a Kano ba.

Gaskiya dama ance Allah wadan naka ya lalace; domin kowayasan lalacewar siyasa a Kano don haka aka cuso wani yaro “stooge” wasi shi Sha’aban Ibrahim Sharada daga wai Billa aka roki Gwamna Ganduje ya sama masa wuri a Municipal don ya zama wakilin majalisar tarayya: Ashe- Ashe anyi haka ne domin tozarta Gwamna Ganduje daga Billa! Wannan kawai kekecine, kila-wa-kala amma yaron irin tutsun da yake yiwa gwamnatin jihar Kano da tsiwar da yake yi tabbas akwai iyayen gidansa wanda a boye suke nuna kiyayya ga Gwamna Ganduje.

Yaron nan yana fadin abubuwa na gabunta kuma yana kashe kudade fiye da kima saboda ya samo daurin gindi sosai wanda yanzu Gwamnan Kano aka turo shi yayi! To wannan alamu ta yadda wannan yaro Sha’aban yake rangwada kasanakwai walakin; yanzu haka ya tsinto wasu wai ‘yan baka suna taya shi cin mutuncin mutane a radiyo, cikinsu shine har da Dauda Kahutu Rarara, mawakin shugaba Buhari, shugaban kasar Nijeriya, shagube da kake yiwa Ganduje cewa Hankaka, kanayi wannan abu amma gaskiya da wanda kakeyi don shi shine dangin Hankaka: Dauda Kahutu Rarara duk sunan da zaka yi, komi dadewarka a duniya, ba zaka kai shata ba, wato Mammalo Shata na Bilki sai dubu ta taru Allah Ya jikansa amin.

Saboda haka juyawa Ganduje baya abune kamar kayi kuma ka gama: Habaici da cin mutunci baya karko ga mai yinsu, wani mawaki yace baya tsoron Allah fiye da wani Sarki, kaga sai buzunsa, to ashe akwai lokacin dashewarsa.

Ayi a hankali Dauda Kahutu Rarara, yaro bari murna karensa ya kama zaki.

Kwamrade Ibrahim Abdu Zango Chairman: Kano Unity Forum, Kano – Nigeria, 08175472298

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *