Rarraba wa ‘yan sintiri makamai: Gwamnan Zamfara ya yi bayanin kare kai

Zamfara ta sanya wa jami’anta takunkumin magana da ‘yan-jarida

Gwamna Bello Matawalle

Tura wannan Sakon

Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da kudirinta na samar da bindigogi dubu 7 domin bai wa ‘yan sintiri da za ta dauko daga al’ummomi domin aiwatar da tsarin da ta kira “Carrot and Stick Approach” domin fatattakar ‘yan bindigar da suka ki mika wuya.

Mai bai wa gwamnan Zamfara shawara kan harkokin yada labarai, Zailani Baffa ne ya bayyana hakan, inda ya ce, matakin da ake kai yanzu a tsarin shi za a ci gaba da yakar wadanda suka bijrie wa sulhu.

A cewarsa, matakin zai shafi dukkan yankunan da yake da matasa, da sarakunansu suka amince mutanen kirki ne. “Gwamnati za ta taimaka masu su samu makamai daga hannun ‘yan sanda irin makaman da gwamnatin tarayya ta yarda wadanda ba irinsu ‘yan sanda ko sojoji ke amfani da su ba.”

Ya ce, ko a ƴan watannin baya-bayan gwamnatinsa ta sanar da burinta na bai wa ƴan jihar da kuma waɗanda ke zaune a jihar damar neman lasisin riƙe bindiga domin kare kansu daga hare-haren masu tayar da zaune tsaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *