Rashin Iyan Zazzau, babban rashi ga kowa -Ya salaam

Iyan Zazzau

Late Iyan Zazzau

Tura wannan Sakon

ISA A. ADAMU Daga Zariya

An bayyana rasuwar Iyan Zazzau, Alhaji Muhammadu Bashari Aminu, tsohon Hakimin Sabon gari a masarautar Zazzau da cewa, babban rashi ne da ya shafi al’umma kafatan ba iyalan mamacin kawai ba.

 Bayanin haka ya fito daga bakin babban sakataren kungiyar ‘yan Lemo a babban kasuwar ‘yan Lemo ta Kwangila da ke Zariya Ustas Ahmad Dayyib Ya Salam, a lokacin da wakilinmu ya zanta da shi, kan rasuwar Iyan Zazzau a kwanakin baya.

Ustas Dayyib Yasalam ya ci gaba da cewa, babu ko shakka rayuwar marigayi Iyan Zazzau Alhaji Bashir Aminu daukacin kungiyoyin da al’ummar karamar hukumar Sabon gari sun amfana da rayuwar marigayin, musamman na yadda ya rungumi kowace kungiya da hannu biyu, a duk lokacin da suka je wajensa.

 Sakataren ‘yan Lemon ya kara da cewa, marigayi Iyan Zazzau shugaba ne nagari da kungiyoyin sa-kai da suke masarautar Zazzau za su dade su na tuna wa da shi, na yadda a kowane lokaci ya jawo hankalinsu na su rinka gudanar da ayyukansu bisa amanar da al’ummar da suke yi masu shugabanci, wadannan shawarwari ya sa kungiyoyin da suke karamar hukumar Sabon gari suka samu daukaka da kuma ci gaba a ayyukan da suke aiwatarwa domin ci gaban wadanda suka zabe su.

 Ustas Ahmed Ya Salam, ya yi amfani da damar da ya samu inda ya yi kira ga daukacin hakimai da suke masarautar Zazzau, da su ci gaba da koyi da marigayi Iyan Zazzau, na rungumar kungiyoyi da hannu biyu tare da tallafa masu, kamar yadda marigayin ke yi a lokacin rayuwarsa, domin su ma a cewarsa, al’umma su amfana da shugabancin su, kamar yadda marigayin ya yi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *