Rashin jaridu a Arewa, abin damuwa-Dokta Braji

Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani

An yi kira ga masu zuba hannun jari da mawadata a Nijeriya ta Arewa da su zuba jarinsu wajen habaka gidajen jarida domin samar da bayanai wajen wayar da kai da ilimatar da al’ummomin yankin.

Kiran ya fito daga babbar daraktar hukumar gudanar da filaye ta jihar Kano, Dokta Zainab Ibrahim Braje a lokacin da ta karbi bakuncin shugaban madaba’ar Triumph, Mallam Lawal Sabo Ibrahim, bisa wakilcin Editan Triumph Mallam Muhammad Hamisu Abdullahi, a yayin da ya kai mata ziyarar nuna goyon baya da taya murna bisa sabon matsayin da ta samu bayan kammala aiki gwamnati a matsayin babbar sakatariya kuma gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya nada ta babbar Darakta a hukumar, a ranar Larabar da ta gabata.

Dokta Braje ta yaba da gudummawar da madaba’ar take bayarwa wajen bayyana kyawawan ayyukan gwamnatin jihar Kano, inda ta kara da cewa, bude gidajen jaridu zai kara karfafar labarai da sakonnin da gidajen radiyo suke bayarwa, wadanda a halin yanzu gidajen radiyo suna da yawa a jihar.

Ta kara da cewa, bangare daya da Arewacin Nijeriya ke kamfarsa a fannin yada labarai shi ne karancin gidajen jarida, inda ta ce, a masaniyarta gidan jaridar Triumph shi ne kadai gidan jarida a jihar Kano, wanda hakan ke nuna karancin gidajen jarida a jihar, kuma abin a duba ne. Daga nan sai ta yi kira ga hukumar madaba’ar da ta kara himmatuwa wajen bayyana ayyukan da madaba’ar ke samarwa, domin al’umma su san irin ayyukan da suke yi.

Ta kuma shawarci madaba’ar da ta rungumi ci gaban zamani da aka samar a bangaren yada labarai da gidajen yada labarai na duniya suke amfani da su, inda ta ce, rumgumar sabon tsarin zai taimaka wa madaba’ar wajen yin gogayya da gidajen yada labarai a ciki da wajen kasar.

Dokta Braje ta kuma yaba da ziyarar inda ta yi alkawarin hada kai da bangaren kasuwanci na madaba’ar wajen bayar da bugun muhimman takardu da kuma tallace-tallace da hukumar ke bayarwa. Tun da farko a nasa jawabin, shugaban madaba’ar, Mallam Lawal Sabo Ibrahim, ya taya ta murna bisa sake nada ta a matsayin babbar darakta ta hukumar gudanar da filaye, inda ya bayyana nadin a matsayin nadin cancanta.

Ya kara da cewa, madaba’ar za ta hada kai da hukumar wajen ganin ta cim ma nasara a dukkanin ayyukanta. Ya bayyana cewa, kasancewar madaba’ar mallakin gwamnati ce, za ta hada kai da hukumomi da ma’aikatun gwamnati wajen yayata manufofin gwamnati ga al’umma, inda ya rufe da cewa, “kasancewar dukkanin manifofinmu su ne mu hidimta wa mutanen Kano iya karfinmu”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *