Rashin kujeru, musabbabin tsadar kudin Hajji –Hamsyl

Hajj 2022

Tura wannan Sakon

Daga Musa Diso

Manajan Daraktan kamfanin Hamsyl Travel and Tours, Alhaji Mustapha Hamisu ya bayyana cewa, rashin wadatattun kujerun aiki Hajji a bana shi ne musabbabin tsadar aikin Hajji a wannan shekara.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke kan titin Ashton, a babban birnin Kano, makon da ya gabata.

Ya ce, a shekarun baya, Nijeriya kusan ita ce ta biyu ko ta daya a duniya wajen yawan mutane da ke aikin Hajji a kasa mai tsarki, domin sama da kujera dubu 100 ake bai wa Nijeriya, amma a bana, kujeru dubu 43 kacal aka bai wa Nijeriya, inda ya bayyana cewa, ba shakka wannan wani babban kalubale ne.

Mustapha ya kara da cewa, a bana sama da mutane miliyon daya ne ake sa ran za su yi aikin Hajji daga sassa daban-daban na duniya, kuma akwai matakai masu kyau da hukumar aikin Hajji ta kasar Makka ta dauka, musamman wajen rage cunkosa da sauyesauye na ganin cewa Alhazan bana sun yi aikin Hajji cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali ba tare da wani kalubale ba.

Daga bisani ya jinjina wa hukumar aikin Hajji ta kasa NAHCON da ta bai wa kamfanoni masu zaman-kansu kujeru 9,300, domin gudanar da aikin Hajjin bana, inda ya ce, wannan ya sanya kamfanoni kamar irin nasu yin tanadi mai kyau ga maniyyata, domin gudanar da aikin Hajjin bana cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Hamisu ya kuma ce, sanin kowane cewa, banbancin kamfaninsu da sauran shi ne gaskiya da da rikon amana.

Daga karshe ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su bi doka da oda a yayin da suke gudanar da aikin Hajjin bana a kasa mai tsarki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *