Rashin nagartar gini, musabbabin rugujewarsa -In ji Kofar Na’isa

Aminu Kofar Na’isa

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

Alhaji Ibrahin Garba Aminu Kofar Na’isa, fitaccen magini kuma hadimi ga al’umma ya ce, ko shakka babu, sana’ar gini tana samar da hanyoyi na dogaro da kai wajen samar da ayyukan yi ga al’umma.

Ya yi tsokacin ne a zantawarsa da wakilinmu a ofishinsa da ke Lokon makera, Kofar Na’isa a birnin Kano. Ibrahim Garba, ya nunar da cewa, a matsayinsa na magini mai tsohon tarihi, mutane masu tarin yawa suna samun dogaro da kai a karkashinsa.

Ya ce, a yanzu haka yana gudanar da ayyukan gine-gine a sassa daban-daban na jihar Kano, sannan dukkanin gine-ginen da kamfanin sa ya yi suna nan garau tun lokaci mai tsawo saboda inganci da kuma kwarewa. Ya kara da cewa, mafiya yawan rugujewar gine-gine da ake samu a duniya yana faruwa ne saboda rashin yin aiki da ingantattun kayan aiki, domin akasarin ruftawa da gine-gine ke yi tana faruwa ne ta sanadiyyar rashin yin amfani da kayan gini masu inganci, wanda hakan yana haifar da asarar rayuka da dukiya a dukkanin lokacin da gini ya rufta.

Kofar Na’isa ya bukaci hukumomi da ke da alhakin kula da harkokin gine-gine da masu ruwa da-tsaki kan harkar gini da kuma kwararru da su kara himma wajen tabbatar da cewa, ana bin ka’idojin yin gine-gine ta yadda za a rinka kauce wa yawaitar ruftawar ginegine musamman a kasashe masu tasowa.

A karshe, ya jaddada cewa, kamfaninsa zai ci gaba da yin ayyuka masu kyau da inganci, kuma a shirye suke da karbar sabon gini ko gyara domin kamfanin nasu kwararre ne kan kowane irin gini da ake bukata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *