Rashin tsaro: Rayuwar mazauna Zamfara babu sadarwa

Rashin tsaro: Rayuwar mazauna Zamfara babu sadarwa

Rayuwar mazauna Zamfara babu sadarwa

Tura wannan Sakon

huaibu Ibrahim daga Zamfara

Mazauna jihar Zamfara sun bayyana halin takura da suka shiga sakamakon katse layukan waya da intanet da hukumomi suka yi.

Hukumomin kasar sun dauki matakin ne da zummar shawo matsalar ‘yan fashin daji da ta addabi jihar. Dumbin jama’ar Zamfara ne a yanzu suke kwarara zuwa makwabtan jihohi domin kiran abokan hulda da ‘yan uwa ta wayar tarho, da sauran aikaceaikacen da katse hanyoyin sadarwa ta haddasa a jihar.

Bayanan da ke fitowa daga Zamfara na cewa, harkokin banki sun tsaya cak, yayin da hada-hadar kasuwanci ta takaita, a wadansu lokuta ma ‘yan uwa kan shiga zullumi saboda rashin ji daga makusantansu da ke sassan jihar. Wadansu Zamfarawa da Albishir ta zanta da su sun bayyana irin wahalar da suke sha tun ranar Juma’a da aka katse sadarwa, kafin su iya kiran waya ko hada-hadar kudi a bankuna.

A cewar wani mazaunin “tun daga ‘yansadau a karamarar hukumar Maru na tafi Funtuwa a jihar Katsina don na yi hada-hadar kudi saboda rashin sadarwa.” Ita ma wata mai sana’a ta intanet da yanzu haka ta yi balaguro zuwa wata jihar, ta ce rashin sadarwar ya yi matukar illa ga cinikin da take samu.

“Harkokina na kasuwancin da nake yi yawanci ina yin su ne a soshiyal midiya. Nakan dora abun da nake sayarwa a Whatsapp da Facebook, ka ga wannan lamari ya shafi rayuwata sosai tun da ba ni da sabis ma to ta ina zan fara?” A wani gefen kuma lamarin ya shafi wadanda ke zaune a wajen jihar ta Zamfara amma saboda matsalar sadarwar ba za su iya jin halin da makusantansu ke ciki ba.

Amma duk da haka da dama sun ce idan har matakin katse sadarwar zai taimaka wa hukumomin fatattakar ‘yan fashin daji, to suna maraba da hakan.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne hukumomi a Najeriya suka katse hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara a wani bangare na fatattakar ‘yan fashin daji da suka addabi jihar.

Kuma kwanaki biyu bayan daukar mataki ne gwamnatin Zamfara ta fitar da sanarwar cewa sojojin Najeriya sun yi luguden wuta a fitattun sansanonin ‘yan fashin dajin da ke fadin jihar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *