Rawa da juyi: Kasar Makka ta amince da Hajjin bana -Fatima Usara

Rawa da juyi: Kasar Makka ta amince da Hajjin bana -Fatima Usara

Rawa da juyi: Kasar Makka ta amince da Hajjin bana -Fatima Usara

Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani Hukumar Alhazai ta Nijeriya, (NAHCON), ta sami labari mai daDi na Dauke dokarhana zirga-zirgar jirage kai tsaye daga Nijeriya zuwa Kasar Makka wanda ya fara tun daga ranar 5 ga Maris na wannan shekarar. Bayanin hakan ya fito ne a sanar- Duba shafi na 2 war da hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Kasa (GACA) ta fitar, inda ta Kara da cewa, an soke dukkanin dokokin da aka saka na hanin zirga-zirgar jirage a sakamakon annobar Korona.

Sanarwar ta Kara da cewa, abin da ake buKata ga maniyyata aikin Hajji da Umarah daga Nijeriya da sauran Kasashen da dokar hanin ta shafa shi ne, shaidar samun cikakkiyar riga-kafin Korona wanda ita ce za ta ba su damar shiga Kasar ta Makka. A sanarwar da shugabar sashin hulDa da jama’a ta hukumar Alhazai ta Kasa, Fatima Sanda Usara ta fitar, ta ce, a bisa dalilin ne, shugaban hukumar, Alhaji Zikirullah Kunle Hassan ya taya al’ummar Musulmi na duniya murna musamman na Nijeriya bisa gagarimin ci gaban da aka samu, inda ya yaba wa Sarkin mulukiyar Makka, Mai alfarma Salman Dan Abdul’aziz da kuma Yarima mai jiran gadon milkin Kasar, Muhammad Dan Salman bisa jajircewarsu wajen ganin komai ya inganta duk da Kalubalen da ake ciki.

Shugaban ya bayyana fatansa na ganin an bude damar gabatar da aikin Hajjin bana, sannan ya yi amfani da wannan damar wajen sanar da jama’a cewa, za a sanar da maniyyatan Nijeriya da zarar hukumar ta gama sanya hannu kan yarjejeniya a tsakaninta da hukumar kula da aikin Hajji da Umarah ta Kasar Makka.

Alhaji Zikirullah Hassan ya kuma jad dada kiransa ga maniyyatan Nijeriya da su kasance masu bin doka da oda a duk lokacin da suka shiga Kasar Makka domin yin aikin Hajji ko Umarah, inda ya yi kira ga maniyyatan da su sani cewa, duk wanda yake son yin aikin Hajji ko Umarah da ya tabbata ya karbi cikakken riga-kafin Korona domin kare kansa da sauran al’ummar Kasar ta Makka. Ya kuma gargadi maniyyata da su kaucewa tafiya Kasar ta Makka da abubuwan da aka haramta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *