Rigimar filin noma: Alkalin kotu ya yi kullikurciya

Alkalin kotu ya yi kullikurciya
Isa A. Adamu Daga Zariya
Rashin zaman mai shari’a Kabiru Dabo, ya kawo cikas na ci gaba sauraron shari’ar da al’ummar Gyallesu suka kai rudunar sojojin Nijeriya da ke Zariya na hana su ci gaba da noma gonakinsu da suka gada daga kakanninsu shekaru fiye da dari da suka gabata.
A sauraron karar da mai shari’a Kabiru Dabo ya yi a watannin baya, a cewar Lauyan da ke wakiltar al’ummar Gyallesu a karar, Barista M.T.Abubakar, kotun ta bai wa rundunar sojojin Nijeriya umurni a rubuce, su daina jan garu, da nufin zagaye gonakin al’ummar Gyallesu da kuma barinsu, da su ci gaba da noma gonakinsu, kamar yadda yadda suka sa ba shekaru da dama da suka gabata.
Lauya Abubakar ya ci gaba da shaida wa wakilinmu cewa, rundunar sojojin sun tsaya da zagaye gonakin al’ummar Gyallesu, kamar yadda kotu ta ba su umurni, amma maganar da kotu ta yi a rubuce ga sojojin na su bar manoman su ci gaba da noma gonakisu, sojojin ba su bi umurnin kotun ba, inda suka ci gaba da hana al’ummar Gyallesu noma gonakinsu, da farko, kamar yadda Lauya Abubakar ya ce, sojojin da kansu suka yi feshin kashe ciyawa da ya zama silar kashe daukacin abubuwan da al’ummar suka shuka ya kone baki daya.
Wata matsala kuma kamar yadda Barista Abubakar ya ce, sojojin sun hana manoman shiga gonakinsu, ga wadanda suka shiga ma a kan rashin sani, sojojin na ci ma su mutunci da ya hada da duka da sauran nau’in wulakanci daga sojojin.
Zuwa hada wannan labari, al’ummar Gyallesu fiye da dubu biyu na cikin matsalolin yadda za su gudanar da rayuwarsu, musamman na yadda za su noma abin da za su ciyar da iyalansu, kasancewar ba su da wata sana’ar da ta wuce noma.
Barista MT Abubakar ya shaida wa wakilinmu cewar, an dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 23 ga watan Fabarairun shekarar 2022 da za a ci gaba da sauraron karar a gaban mai shari’a Kabiru Dabo.