Rigimar sojoji, manoma ta kai kololuwa: Manoma na bukatar Sarkin Zazzau, gwamna su sanya baki

Tura wannan Sakon

Isa A. Adamu Daga Zariya

Mutanen garin Bomo da sauran garuruwan da suke kewaye da gundumar Bomo sun mika kukansa a rubuce ga gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i da mai martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli kan matsalar da ke tsakaninsu da sojojin Nijeriya a Basawa kan hana su noma gonakinsu na tsawon lokaci.

Bayanin haka, ya fito ne daga shugaban kungiyar da suka mallaki gonakin, Alhaji Surajo Musa Bomo, inda ya shaida wa wakilinmu cewar, tuni suka mika takardunsu na koke ga wadanda aka ambata, domin su shiga maganar tsakanin sojojin da aka ambata.

Alhaji Surajo ya ci gaba da cewa, a watannin baya bayan koken da suka gabatar ga gwamnan jihar Kaduna kan matsalar gonakinsu da suka gada shekaru fiye da 100 da suka gabata, sai gwamnan jihar Kaduna ya kafa kwamitin da ya zauna da wakilan al’ummar Bomo da kewaye da wakilan sojojin Nijeriya da wakilai daga ma’aikatar kula da kananan hukumomi ta jihar Kaduna bisa jagorancin shugaban karamar hukumar Sabon gari, Injinya Mohammed Usman.

A zaman da aka yi a cibiyar karamar hukumar Sabon Gari, al’ummomin Bomo da wakilan sojojin Nijeriya, a cewar Alhaji Srajo Bomo, kowane vangare ya yi jawabi, wanda a karshe, shugabannin kwamitin da gwamnan jihar Kaduna ya nada su, suka bayyana cewa, za su bayyana abubuwan da aka tattauna a wajen taron, tare da mika wa gwamnan jihar Kaduna rahoton zaman da aka yi a tsakanin wadanda aka ambata, domin shi kuma gwamnan, ya dauki matakan da suka dace.

A zaman da aka yi, a cewar Alhaji Surajo Bomo, kwamitin ya yi gargadi ga kowane vangare na al’ummar Bomo da kewaye da kuma sojojin da su dakatar da kowane batu a tsakaninsu a kan gonakin da ake cece-ku-ce a kansu, har lokacin da gwamnatin jihar za ta fitar da matsayinta kan wanda ya mallaki gonakin a tsakanin wadanda aka ambata, sai aka wayi gari, sojojin suka fara haka rami, domin zagaye filayen gonakin da al’ummar Bomo suka mallaka, kamar yadda aka bayyana a baya. Alhaji Surajo Bomo ya ci gaba da cewa, ganin haka ramin da sojojin suka yi, sai suka kara rubuta kokensu ga gwamnan jihar Kaduna da kuma mai martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli domin nuna damuwarsu na matakan juya wa umurnin kwamitin da sojojin Nijeriya suka yi, na ci gaba da haka ramin, domin katange gonakin da aka ambata.

Shugaban kwamitin Alhaji Surajo Bomo ya nanata kukansa ga gwamnan jihar da mai martaba Sarkin Zazzau, da su duba matsalar da kuma halin da al’ummar Bomo da kewaye ke ciki, na hana su noma da sojojin suka yi da kuma fara rushe masu gonakinsu.

Da kuma Alhaji Surajo Bomo ya juya ga al’ummar Bomo, ya umurce su da su ci gaba da bin doka da tattalin zaman lafiya da aka san su da shi, musamman yadda gwamnan jihar da mai martaba sarkin Zazzau suka lashi takobin duba koken al’ummar Bomo da kewaye, daga lokacin da aka kafa kwamitin a watanni kadan da suka gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *