Rike sana’a da gaskiya kan taimaka wa dankasuwa -Ibrahim Tarauni

Daga Rabiu Sunusi
An hori Yankasuwa dasu zama masu kamanta gaskiya da tsoron Allah yayin gabatar da harkokin kasuwancinsu koda yaushe.
Shugaban kungiyar masu gyaran kaji da sai kajin na kasuwar karamar hukumar Tarauni awata zantawa da ALBISHIR.
Tarauni yace lallai kodayaushe idan Mai sayen kayanka yazo yaga kakamanta mashi yayin gudanar da wannan kasuwanci asakaninka dashi zai kara bashi kwarin gwuiwa dan gobe yadawo. Shugaban yakuma kara dacewa kasancewar Sanaar gyaran kaji tana biya masu bukatunsu na yau da kullum sabanin zaman banza da baida wani amfani.
Haka Kuma kasancewar su mafi yawancin masu wannan sana’ar ma tasane Kuma masu iyali wanda dahaka suke biyan bukatun yaransu na karatu da al’amuran yau da kullum.
Yakuma kara Jan hankalin abokan sana’arsa cewa sukara azama wajen kamanta gaskiya ayayin kasuwanci su day mutane ta kowace fuska Kuma su zauna lafiya da kowa babu tashin hankali.
Ibrahim Yakima yaba da irin gudunmuwar da ma’aikatar kula muhalli ta jahar Kano awani tallafin kayan aiki data ba wannan kungiya dan cigaba da tsabtace gurin sana’arsu kamar yadda yakamata tare da Gina masu gurin sana’a datayi Kazalika yakuma bukaci gwamnati jahar kano karkashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje data taimaka masu da kayan aiki nazamani kamar yadda wasu guraren suka samu dan samun saukin aikinsu.
Yakuma tabbatar da cewa yazuwa yanzu Wanda sukecin abinci awannan harka sunfi mutum dari da hamsin idan akai jimilla akullum.
Daga karshe yace samun hadun kai na abokan sana’a na kan gaba wajen nasarar dasuke ganin sun samu atafiyarsu.