Rikici a Sudan ta Kudu: Fiye da mutane dubu sun salwanta

Kwamitin tsaro na majalisar Dinkin Duniya ta ce, fiye da mutane dubu suka rasa rayukansu cikin watanni shida, yayin da aka sace aqalla mutane 400 sakamakon rikice-rikicen qabilanci a Sudan ta Kudu.
Har yanzu Sudan ta Kudu na qoqarin murmurewa daga rikicin tsawon shekaru shida wanda ya tilasta wa gwamnati rarraba madafun iko a cikin watan Fabairu 2020, matakin da ya kawo qarshen tashin hankalin.
A baya-bayan nan dai, rikici ya tsananta tsakanin qabilu a qasar sakamakon dalilai mabambamta da suka hada da barnar da shanu ke yi wa manoma.
Babban Jami’in Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Sudan ta Kudu, Dabid Shearer ya ce, fiye da mutane dubu suka mutu a garin Warrap a cikin watanni shida kuma a yanzu haka akwai mutane da dama da suka yi azamar qaddamar da hare-haren daukar fansa a cewarsa.
Jami’in ya yi gargadin cewa, rikicin qabilancin ka iya qazancewa da zarar an shiga lokacin rani nan da watan Janairu.
A can kuwa gabashin Jonglei, daruruwan mutane ne suka mutu a rikicin, sannan fiye da mutane 400 aka
sace su, kuma akwai yiwuwar nan gaba kadan, tashin hankalin ya yi qamari a Jonglei a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Masu sanya ido sun yi gargadin cewa, rikicin qabilancin na yin barazana ga yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cim ma a cikin watan Satumban shekarar 2018 domin kawo qarshen yaqin da ya laqume rayuka kusan dubu 400 a qasar.
mance, shekaru 40 da suka wuce.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin, Wang Wenbin ya fada a wani taron manema labarai cewa, lallai qasar na taya Joe Biden da Kamala Harris murnar lashe zaben.
Kafin yanzu, Sin na cikin wadansu manyan qasashen da ba su taya zababben shugaban Amirka murna ba kamar su Rasha da Medico.
Tun da kafafen yada labran Amirka suka sanar da wanda ya samu quri’u mafi yawa a zaben shugaban Amirka, shugaba mai barin gado Donald Trump bai amince da shan kaye ba akasin yadda aka saba yi a qasar.