Rikicin Dangote,Kogi: Gwamnatin tarayya ta shiga tsakani

Rikicin Dangote,Kogi
Tura wannan Sakon

Gwamnatin Nijeriya ta shiga tsakanin rikicin da ya kunno kai tsakanin gwamnatin jihar Kogi da kamfanin hamshakin attajirin Afirka, Aliko Dongote, dangane da mallakar katafaren kamfaninsa na siminti da ke Obajana.

Bayanai sun ce, an gana tsakanin shugaban rukunonin kamfanin na Dongote da kuma gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello da kuma takwaransa na jihar Nasarawa, Abdullahi Sule. Yunkurin sulhun da gwamnati ta yi, ya zo ne, bayan matakin da gwamnatin Kogi ta dauka na rufe katafaren kamfanin simintin Obajana, bisa zargin kaurace wa biyan haraji, da kuma rashin fayyace gaskiyar hakkin mallakar kamfanin.

Wadansu majiyoyi sun ruwaito cewa, shugabannin rukunin kamfanonin na Dangote sun kammala shirin tunkarar kotu a wannan makon kan al’amarin, ciki kuwa har da yadda ‘yan banga na gwamnatin jihar Kogi suka kai farmaki kan katafariyar masana’antar simintin da ke Obajana, inda ake zargin sun jikkata ma’aikata da dama tare da rufe kamfanin.

A ranar Alhamis ta makon jiya, gwamnatin jihar Kogi, ta gabatar da rahoton kwamitin kwararru na musamman kan tantance halaccin mallakar kamfanin simintin na Obajana.

Yayin gabatar da rahoton, sakatariyar gwamnatin jihar ta Kogi, uwargida Folashade Ayoade ta ce, ba a bi ka’ida ba wajen mika Obajana zuwa kamfanin Dangote.

Haka zalika, wadansu takardun shaida guda uku da suka tabbatar da cewa, gwamnatin Kogi ce ta mallaki kamfanin simintin na Obajana, an yi amfani da su wajen karbar bashin Naira biliyan 63 da Dangote ya yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *