Rikicin fili: Kauran Bauchi ya fusata Musulmin Bauchi

Idan masalaha ta gagara, ba na tsoron bugawa da kowa -Bala Mohammed

Bala Mohammed

Tura wannan Sakon

Musulmin da ke unguwar Yolan Bayara cikin garin Bauchi sun rubuta takardar korafi kan matakin da gwamnatin jihar ta dauka na bai wa Kiristoci wani katafaren filin makabarta da Musulman suka ce mallakinsu ne.

Musulman sun rubuta wasikar koken nasu a ranar 10 ga Janairu, 2023 zuwa gwamnan jihar, Sanata Bala Mohammed ta wasidar Sakataren gwamnatin jihar.

A cikin wasikar, an kuma yi kwafin hukumomin tsaron jihar da Sarkin Bauchi da shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam, reshen jihar Bauchi da shugaban kungiyar Izala ta JIBWIS, reshen jihar Bauchi, inda Musulman suka bukaci daukar matakin gaggawa domin hana barkewar rikici tsakanin al’ummar jihar.

Da yake mayar da martanin gaggawa, mai magana da yawun gwamnan jihar Bauchi, Mukhtar Gidado ya bayyana cewa, kawo yanzu gwamnati ba ta mika filin ba mai fadin kadada 470 ga Kiristocin, yana mai cewa, har yanzu, gwamnati na ci gaba da nazari kan lamarin.

A makon jiya ne, Kiristoci karkashin jagorancin shugaban kungiyar CAN a Bauchi, Rabaran Dokta Abraham Demius Damina, ya bayyana cewa, gwamnan jihar ya ba su kyautar fili mai fadin kadada 50 domin amfani da shi a matsayin makabarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *