Rikicin gonaki tsakanin, Bomo da sojoji: Gwamna el-Rufa’i ya cancanci yabo -Alhaji Yahuza

Kaduna ta ciyo bashi har wuya -PDP
Tura wannan Sakon

ISA A. ADAMU Daga Zariya

An bayyana matakan da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed ElRufa’I ya dauka na kafa kwamiti domin kawo karshen matsalolin wa ke da mallakar fili a tsakanin al’ummar Bomo da suke karamar hukumar Sabon gari da rundunar Sojojin Nijeriya da cewar abin a yaba wa gwamna ne.

Wani shugaban al’umma a Samaru mai suna Alhaji Yahuza Suleiman Dan Sa’a ya bayyana wannan yabo alokacin da ya gana da wakilinmu da ke Zariya kan kwamitin da gwamna El-Rufa’I ya kafa domin sauraron ko wane bangare, da kuma kwamitin ya kunshi manyan ma’aikata daga ma’aikatar kula da kananan hukumomi na jihar Kaduna da wakilan mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli da wakilan a’ummar Bomo bisa shugabancin wakilin al’ummar da suka mallaki filayen da ake takaddama a kansu mai suna Alhaji Surajo Bomo.

AlhAJI yahuza Suleiman ya ci gaba da cewar, babu ko shakka, yadda mai girma gwamnan jihar Kaduna ya saurari al’ummar Bomo bayan sun rubuta takardar koke gareshi, a cewarsa, al’umma Bomo dole su nuna matukar jin dadinsu ga mai girma gwamna na matakin da ya dauka, na umurtar shugaban karamar hukumar Sabon gari Injiniya Mohammed Usman ya shugabanci wannan kwamiti da aka nada.

Shugaban al’uumar ya ci gaba da cewar, al’ummar Bomo ya ci gaba da bin doka da odar hukuma, ba su da niyyar daukar doka a hannu, na yadda suka wayi gari, filayensu da suka gada kaka – da – kakanni, rundunar sojojin Nijeriya ta ce wannan makeken fili, iya ganin ka, suka ce mallakarsu ne.

Alhaji Suleiman Dan Sa’a ya kara da cewar, a kwai lokacin da sojojin suka sa ma su harajin sai sun biya Naira dubu Ashirin a ko wane kadada daya, kafin su barsu su noma gonakinsu, amma duk da matsalolin da suka fuskanta, a cewar Alhaji Yahuza, bas u dauki doka a hannunsu ba, domin, kamar yadda ya ce, al’ummar Bomo su na da yakinin in har wannan matsala ta je ga kunnuwar gwamnan jihar Kaduna, matsalar za ta kawo karshe.

Da kuma Alhaji Yahuza ya juya ga ‘yan kwamitin, a nan sai ya yi kira garesu, da su mika wa mai girma gwamna rahoton tattaunawar da suka yi da al’ummar da aka ambata da kuma wakilin rundunar sojojin Nijeriya da yakasance a wajen taron na kwamitin da gwamna ya kafa, domin gwamna ya dauki matakan da suka dace, ta yadda al’ummar Bomo da sauran al’umma za su sami sa’idar matsalolin da suke fuskanta a tsakaninsu da rundunar sojojin Nijeriya.

Da kuma ya jiya ga shugaban kwamitin kuma shugaban karamar hukumar Sabon gari, I NJINIYA Mohammed Usman, ya nuna matukar gamsuwarsa na yadda ya bi duk matakai da kuma hanyoyin da suka dace, domin kawo karshen matsala, kamar yadda Hakimin Bomo Madakin Zazzau Alhaji Muhammad Munnir Jafaru ya dauka, amma wutar matsalar ba ta mutu a hannunsu ba.

A karshe, Alhaji Yahuza Suleiman Dan Sa’a, ya nanata kira ga al’umma Bomo, da su ci gaba da bin doka, su guji daukar doka a hannunsu, a kan wannan matsala da suke ciki da aka kwashe shekaru da ya waba ta mutum ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *