Rikicin Malaman Kano: Imam Alhamidi ya yi gum

Sheikh Ibrahim Khalil
Daga Salihu S. Gezawa
Majalisar Malamai ta kasa rashen jahar Kano ta shiga wani yanayi na shugabancinta inda har aka samu tsagin Pakistan a kwanakin baya ya bayar da sanarwar tsige shugabanta na jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil tare da maye gurbin sa da Dokta Saleh Pakistan.
Sai dai a lokacin da tsagin Pakistan ke bayar da wancen umarni a jihar, sai aka jiyo Dokta Sa’idu Ahmad Dukawa na magana da yawun wani vangare na Malamai na cewa, su har yanzu Sheikh Ibrahim Khalil suka sani a matsayin shugaban Majalissar Malamai ta jihar Kano yana mai nisanta kansu da wacan matsaya ta vangaren Pakistan.
Al’ummar jihar Kano sun zuba ido da jin wane bangare ne zai rinjaya musamman vangaren Pakistan da suke ganin wajibi ne Khalil ya bar kujerar saboda dalilin su da kuma vangaren da suke ganin ba wani dalili da zai sa Khalil ya sauka kamar yadda Dokta Sa’idu Dukawa ya furta.
Albishir ta hango babban Limamin Masallacin Juma’a na Sarkin Musulmi Abubakar na III da ke babbar kasuwar kayan masarufi ta duniya da ke Gezawa, Ustaz Muhammad Sani Abdallah Alhamidi a sakatariyar Majalissar Malaman jihar Kano har take jin ta bakinsa kan mai zai iya cewa, dangane da danbaruwar shugabancin Malaman, sai ya ce, shi a gaskiyar lamari ba shi da wani ra’ayi da zai iya bayyanawa.