Rikicin shugabancin nakasassu a Kano: Kungiyar nakasassu ta Kasa ta sanya ranar zabe

Kungiyar nakasassu ta Kasa

Tura wannan Sakon

Daga Salisu Baso

Kungiyar nakasassu ta kasa ta rushe jagorancin jihar Kano tare da umartar reshen da ya shirya sabon zabe.

A ganawarsu da ‘yan-jarida a jihar Kano, kwamitin da hedikwatar kungiyar ta kafa domin shawo kan rikicin shugabancin da ‘yan kungiyar ke fama da shi, a karkashin Barista Haruna Musa da sakataren kwamiti, Mista Olatunji, ya amince da gabatar da zaman da ‘yan kungiyar suka yi na gudanar da sabon zabe a ranar 16 ga Yuli 2022.

Ya ce, taron da kwamitin ya yi da wakilan kungiyoyin nakasassu guda shida da suka hada da makafi Guragu da kutare da kurame da masu larurar laka da zabiya karkashin jagorancin babban sakataren hukumar kula da nakassasu ta kasa, Mista James Lalu da wakiliyar sakataren gwamnatin jihar Kano, Hajiya Bilkisu Ibrahim Khalid  da babban sakataren Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano  Kwamared Sale Jili da wakilin shugaban kungiyar nakasassu ta kasa sun amince da kuma zartar da rushe shagabanci na hadaddiyar kungiyar nakasassu a jihar Kano, saboda wadanda ke jagoranci ba a zabe su bisa doka ba.

Har ila yau, zaman ya amince da sanya ranakun 14 zuwa 16 ga Yuli cewa, dukkan bangarorin za su bayar da sunayen wakilan su da za a kafa kwamitin zabe kuma za su mika suanayen ga ofishin shugaban hukumar agajin gaggawa na jihar Kano, inda da zarar an kafa kwamitin zabe za a tattara sunayen wakilan kananan hukumomi da za su yi zabe.

Barista Musa ya kuma cewa, masu ruwa da tsakin sun amince da sanya ranar 16 ga Yuli 2022 ta zama ranar zabe.

Da yake jawabi babban sakataren hukumar nakasassu ta kasa, Mista James Lalu ya bayyana kafa kwamitin sulhu da cewa, ganin mahimmancin jihar Kano a hadaddadiyar kungiyar nakasassu ta kasa ya sanya dukkan masu ruwa da tsaki na kungiyar suka taru a Kano domin shawo kan barakar da da ta taso.

Daga nan ya gode wa dukkan bangarorin saboda hadin kai da goyon baya da suka bayar na kawo karshen sa-in-sar da ta taso, haka ya tabbatar da shirin hukumarsa na sanya kyautatuwa da jindadin nakasassu a fadin kasar a karkashin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Ya roke su da tabbatar da zaman lafiya a tsakaninsu domin ci gaban nakasassu kuma ya gode wa shugabannin kungiyoyinsu.

Shi ma babban sakataren hukumar agajin gaggawa ta jihar Kano, Kwamared Sale Jili ya tabbatar da ganin an gudanar da zabe mai inganci da bai wa kowane bangare hakkin sa domin ci gaban nakassau a jihar Kano, inda ya jaddada goyon bayan gwamnatin jihar Kano karkashin gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje kan inganta rayuwar nakassassu a jihar. Ya kuma roke su da su tabbatar sun yi katin zabe domin sauke hakkinsu na kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *