Romon dimukuradiyya: Gwamnan Bauchi ya gwangwaje Dass, Toro da tallafi

Idan masalaha ta gagara, ba na tsoron bugawa da kowa -Bala Mohammed

Bala Mohammed

Tura wannan Sakon

Jamilu Barau Daga Bauchi

A jihar Bauchi an kaddamar da rabon kayayyaki domin cin moriyar dimukradiya a karkashin shirin da ya sanyawa suna Kaura Economic Empowerment program K.E.E.P wanda ya gudana a garuruwan Dass da Toro ta jihar Bauchi.

Wadannan kananun hukumomi su ne na 12 da aka gudanar da rabon kuma za a ci gaba da rabon a sauran 8 da suka rage nan gaba in Allah ya yarda.

A lakacin da yake jawabin kaddamar da rabon, gwamna Kaura ya ce, mulkinsa ya zo ne da tsarin samar da sauki, ko rage radadin talauci ga al’umma da bayar da gudumawa ga mata da matasa ta hanyar samar masu da tallafi na kasuwanci domin dogaro da kansu.

A bayanin na sa ya ce, zuwa yanzu haka a karkashin mulkinsa da kuma tsarin nan da ya samar na K.E.E.P an bai wa dubban mata da matasa jari da kayan sana’a wanda zai habaka kasuwancinsu musamman ma a karkara.

Ya kara da cewa, fiye da Naira milliyan 75 aka kashe a kowace karamar hukuma a kananun hukumomi 20 da muke da su a fadin jihar. Gwamnan ya yi kira ga wadanda suka amfana da tsarin da su yi murna kana su yi amfani da abin da aka ba su ta hanyar da ya dace.

Sannan ya kara gaya wa mahalarta taron bikin cewa, a cikin tsarin mulkinsa zai ci gaba da samar wa jihar abin misali ko koyi a tsarin shugabanci a idanun takwarorinta.

Ya ce, ga misali na hanyoyi da suka tashi daga MararrabaGumau, Rishin-Tulu, da Rimin Ziyam ya hada da Palama an yi su baki daya. Daga karshe, ya kara da kiran ‘yan jiha da su ci gaba da mara wa tsarin gwamnatinsa baya domin ganin ta kai ga idah komai cikin nasara, kamar manyan hanyoyi da gyare gyare da gine gine na cibiyoyin lafiya.

Cikin jawabinta a filin taron, matar gwamna Hajiya Aisha Bala Muhammad ta yaba wa gwamnan bisa tsarin da ya kawo wanda ya bayar da ci gaba na alheri a fadin jihar Bauchi, kuma ta yi kira ga wadanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da shi ta hanyar da ya dace domin habaka tattalin arziki da zai kawo ci gaba a jiharmu ta Bauchi.

A jawabinsu na godiya a madadin al’ummar yankin, kwamishinan da masu ruwa da tsaki da shuwagabannin kananun hukumomin 2 sun yaba wa gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin gwamna Kaura bisa dimbin alheri da aka kawo masu a yankinsu.

Sannan sun yi kira ga wadanda suka sami tallafin da su yi godiya, su ci gaba da mara wa gwamnati mai ci baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *