Ronaldo ya ci kwallo ta 136 a Champions League

Ronaldo ya ci kwallo ta 136 a Champions League

Ronaldo ya ci kwallo ta 136 a Champions League

Tura wannan Sakon

Cristiano Ronaldo ya ci kwallo na 136 a gasar Champions League a wasan da Young Boys ta ci Mancheter United 2-1 ranar Talata. Ronaldo ne ya fara cin kwallo minti 13 da fara tamaula, inda Young Boys ta farke ta hannun Nicolas Moumi Ngamaleu a wasan na rukuni na shida.

Daf da za a tashi Young Boys ta kara na biyu ta hannun Jordan Siebatcheu da hakan ya sa ta hada maki uku a karawar. A wasa 68 da ya buga a Champions League tun bayan da ya cika shekara 30 da haihuwa, Ronaldo ya ci kwallo 63, jumulla yana da 136 a raga.

Hakan ya sa yana kan gaba da tazarar 35 tsakanin ‘yan wasan da suka kai shekara 30 ko fiye da hakda suka ci kwallo a tarihin Champions League. Lionel Messi dan kwallon Paris St Germain shine na biyu a yawan cin kwallaye a Champions League mai 120 a raga.

United ta karasa karawar da ‘yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Wan Bissaka jan kati. Aaron Wan-Bissaka shine dan wasan Manchester United na farko da aka bai wa jan kati a Champions League tun bayan wanda aka kori Nani a fafatawa da Real Madrid cikin Maris din 2013.

An buga karawar da ‘yan kallo a karon farko a gasar tun bayan 2020, sakamakon bullar cutar korona.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *