Rumfoba ajin 91 ta yi taron cika shekaru 30

Rumfoba ajin 91 ta yi taron cika shekaru 30

Rumfoba ajin 91 ta yi taron cika shekaru 30

Tura wannan Sakon

Daga Ahmad S. Ahmad

Babban Sakatare na uwar kungiyar RUMFOBA ta kasa wanda kuma shi ne mataimakin shugaba na aji 91, Malam Garba Usman Garba ya bayyana cewa, sun yi taron cikar su shekaru 30 da kammala makaranta domin inganta zuminci tsakaninsu, ya ce a baya sun bayar da kyautar litattafai ga hukumar makaranta.

Haka kuma Malam Garba Usman ya kara da cewa, sun nemi a ba su guri a makarantar domin su shuka bishiyoyin zogale adadin shekarun kammala makarantarsu fiye da guda 1000 domni kare hamada da kuma bunkasa tattalin arzikin makarantar.

Da ya koma ta kan inganta ilimi kuwa ya bayyana cewa, za su shuka bishiyoyin Madaci da darbejiya a makarantar domin bincike da koyar da yara sanin mahimmancin su ta yadda hakan zai zama cibiyar bincike da za a rinka amfani da ita ba ma a Kano ba har a kasa baki daya.

Daga karshe, ya bukaci sauran mambobin kungiyar da su ci gaba da tallafa wa ayyukan su domin ganin an samu sakamakon da ya kamata ga daliban da ke karatu a cikin makarantar a halin yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *