Rundunar SAHEL ta kashe mutane 5, ta kubutar da 3

Tura wannan Sakon

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Aci gaba da kokarin kawo karshen ‘yan bindiga sojojin Sahel Sanity suna ci gaba da samun  nasarori a yakin da suke yi da  ‘yan fashi inda suka kashe mutun biyar suka kuma kubutar da mutane da dama ciki har da jarirai a yankin Arewa maso Yamma.

Hakan ya fito ne cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a yau, wanda mukaddashin Daraktan ayyukan yada labarai, Birgediya Janar Benard Onyeuko ya sanyawa hannu, ya ce  an samu nasarorin ne a ayyukan da aka yi a baya-bayan nan “A ranar 29 ga Oktoban 2020, sojoji suka amsa kiran gaggawa a kauyen Diskuru da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina”.

Ya ce ‘yan fashin sun afka wa kauyen ne kan babura, suna harbe harben kan mai uwa da wabi da nufin tsoratar da mazauna yankin tare da wawushe abubuwa da dama, sai da sojojin sun gwabza da masu  kai hare-haren tare da tilasta musu janyewa a cikin yakin.

Sakamakon artabun sojojin sun kashe ‘yan fashi da makami uku kamar yadda ake zaton wasu da dama sun tsere da raunuka daban-daban na harbin bindiga, Inji Onyeuko.

Ya bayyana cewa, a kan hayarsu ta jayewa  an gano karin gawarwakin Biyu, “Bayan artabun, an kubutar da mata uku da jariransu da ‘yan ta’addan suka sace “ ya ce  an kashe soja guda a kokarin kubutar da daya daga cikin uwayen da ke jinya a yayin artabun.

Ya  kara da cewa, sojoji da aka tura kauyen Dan Ali suna aiki da ingantaccen bayani sun kame mutane 2 da ake zargin ‘yan fashi da makami ne wadanda suka hada da Samaila Usman da Idi Bello”.

 Domin haka an yaba wa jaruman sojojin na Operation SAHEL SANITY saboda jajircewansu, sun kuma tabbatar wa mutanen yankin na Arewa maso Yamma kan kudurinsu na kare rayuka da dukiyoyin da ke yankin.

“An kuma karfafa musu gwiwa su baiwa sojojin ta hanyar samun ingantattun bayanai  kan lokaci wanda zai taimaka wajen gudanar da ayyukansu” inji Janar Onyeuko.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *