Rundunar ‘yan-sanda ta bude sabon ofishin kwamanda na Shinkafi

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Babban Sufeton ‘yan sanda (IGP), Muhammad Adamu, ya kaddamar da sabon ofishin kwamandan yanki a garin Shinkafi, a karamar hukumar Shinkafi da ke Zamfara.
Hakan ya fito ne daga jami’in hulda da jama’a na ‘yan-sanda na jihar, SP Muhammad Shehu, a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Gusau.
Ya kara da cewa, sabon ofishin wanda Hedikwatar rundunar ’yan sanda ta gina kwamishinan‘ yansanda na jihar, Mista Abutu Yaro ne ya bude shi a madadin IGP.
Ya ce, aikin yana daga cikin kudurin da gwamnatin tarayya ke da shi na samar da kyakkyawan yanayin aiki ga jami’an ‘yan sanda don su sami damar sauke nauyin da ke kansu na kiyaye lafiyar jama’a, domin samar da zaman lafiya, da tsaro a fadin kasar.
“IGP yayi kira ga jami’an ‘yansanda da mazaunan yankin su yi amfani da ofishin yadda ya kamata da kuma abubuwan da aka samar a ciki.
Shehu ya ci gaba da yin kira ga al’ummomin yankin da ma sauran yankunan, da su nuna godiya ga wannan aikin ta hanyar tallafa wa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a kokarin da suke yi na shawo kan matsalolin tsaro da ke addabar jihar, “in ji Shehu.
Shugaban ‘yansanda na jihar zamfara, CP Yaro, wanda tun da farko ya ziyarci sarakunan Zurmi da Shinkafi a wani bangare na ziyarar fahimtar juna da ya yi wa sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a jihar.
Ya gode wa masarautun biyu kan yadda suke aiki tare da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin, ya ce “Ina neman karin goyon baya daga gare ku a wannan batun,” in ji CP .
A yayin ziyarar, ya yi jawabi ga jami’an ‘yansanda na rukunin Yankin Shinkafi da Zurmi da Ofisoshin ’Yan sanda na Shikafi, da kuma ’yan sanda na Musamman da gwamnatin jihar ta dauka kwanan nan.